Ferfesa Bichi Ya Yi Ta’aziyya Ga Sarikin Katsina Bisa Rasuwar Sarkin Sulluɓawan Katsina.
Mataimakin Shugaban jami’ar Dutsinma ta gwamnatin tarayya na yin ta’aziyya ga sarkin Katsina Dr. Abdulmummuni Kabir Usman bisa rasuwar sarkin Sullubawan Katsina hakimin Kaita Abdulkarim Kabir Usman.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na jami’ar Habibu Umar Aminu.
Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi wanda shi ne ke riƙe da sarautar Wazirin Malaman Katsina wadda sarkin Katsina ya naɗa shi, ya bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi ga kasar nan.
Ya kuma roki Allah SWA ya jiƙanshi da rahama, tare da ba iyalanshi hakurin jure rashin.
Alhaji Abdulkarim Kabir Usman ya rasu yana da shekaru 68 a ranar Juma’a 8 ga watan Afirilun wannan shekarar ta 2022, kuma ya bar matan aure 2, da ‘ya ‘ya 37.
Kafin rasuwarshi, shi ne sarkin Sullubawan Katsina hakimin Kaita.
