Gwamnatina Zata Cigaba Da Hada Kai Da Hukumomi Domin Inganta Ayyukan Ban Ruwa a jihar Bauchi –Bala Muhammad
Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed yayin da yake karbar bakuncin masu ruwa da tsaki na Hukumar Raya Kogin Hadejia Jama’are (HJRBDA) a wata ziyarar da suka kawo masa gidan Gwamnatin jihar Bauchi.
Gwamna Bala wanda ya yaba da shirye-shiryen da Hukumar ke aiwatarwa, ya kuma yi kira da a kara kokari wajen samar da ayyukan ban ruwa a a jihar Bauchi Domin inganta Noma a fadin jihar .
Dakta Bala Muhammad ya bayyana cewa hakika albarkatun ruwa da madatsu da ake ban ruwa da su hakika babban ga cigaban kasa ne domin da samun madatsun ruwan ne kawai manoma ke tsayuwa suyi noma rani da damuna kuma a samu yanayin kiwo mai kyau.
Gwamna Bala ya kara da cewa gwamnatin sa shirye take ta ba da hadin kai ga (HJRBDA) da sauran masu ruwa da tsaki a harkar kula da albarkatun ruwa domin farfado da duk wani shirin ban ruwa da aka yi watsi da shi a jihar.
Haka kuma ya cigaba da cewa jihar Bauchi karkashin gwamnatin sa shirye take ta hada kai da gwamnatin tarayya don kara farfado da fannin kiwo domin amfanin al’umma da gwamnatin jihar Bauchi.
Manajan Daraktan Hukumar, Alhaji Ma’amun Da’u Aliyu ya ce sun kawo ziyarar ne domin neman goyon baya da hadin kan gwamna Bala Muhammad da, hukumar su ta (HJRBDA) domin gudanar da ayyuka masu inganci kan nauyin da aka dora musu.
Ya ce hukumar za ta aiwatar da ayyukan ban ruwa a kananan hukumomin Misau, Ningi, Katagum, Darazo da Jama’are domin magance dukkanin kalubalen da ake fuskanta.
