September 18, 2026

Zaban Kananan Hukumomi: Zamu Fito Bakin Rai Bakin Fama -Jam’iyyar PDP A Katsina

0

Daga Wakilinmu

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Katsina, Hon. Salisu Yusuf Majigiri ya jagoranci zama na musammna da dukkan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a jihar Katsina domin yanke hukuncin shiga zaban kananan hukumomi mai zuwa

Majigiri wanda ya kara tabbatar wa da ‘ya’yan jam’iyyar na PDP cewa za a shiga zaben da za a gudanar na kananan hukumomin jihar Katsina, wanda gwamnatin jihar Katsina da hukumar zabe ta jihar Katsina suka bada sanarwar gudanarwa nan da watan Afrilu mai zuwa.

Hon. Majigiri ya nemi yardar ‘yan jam’iyyar na PDP akan amincewar su don ganin an shiga wannan zabe kuma sun amsa masa da cewa tabbas sun aminta, kuma a shirye suke don ganin cewa an fito bakin rai bakin fama har a cimma nasara insha Allah.

Sannan ya yi kira ga dukkan masu sa ido na duniya akan su sanya ido game da wannan zabe, musamman yadda wannan jihar ta kasance jihar shugaban kasa.

“Rashin gudanar da sahihin zabe shi zai tabbatar mana da cewa shugaban kasa ba adali ba ne, domin kuwa idan har bai sanya aka yi zabe ingantacce ba to tabbas kimar shi za ta ida zubewa”. Inji shi

Daga karshe Hon. Majigiri ya yi kira da babbar murya ga al’ummar jihar Katsina, musamman ‘yan jam’iyyar PDP cewa wannan zaben da za a gudanar shi ne matakin farko na fita kuncin da jam’iyyar APC ta jefa su a ciki.

Dan haka duk yadda za suyi don ganin cewa sun maido martabar su to suyi, idan kuwa suka kwanta aka yi masu abinda ba daidai ba to sun dai san halin da suke ciki

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *