September 17, 2026

Dalilin Da Yasa Ba Zan Yi Takarar Shugabancin Karamar Hukumar Kankia Ba

0

Daga Nasiru Hassan Ma’ajin Kankia

Da sunan Allah (SWT), ina godiya kwarai da gaske da dukkan shawarar da na samu anan da kuma a zahiri daga abokan arziki da sauran yan’uwa.

A dalilin haka ne na janye tunanin neman takarar karamar hukuma bisa ga dalilai da dama muhimman sune:

1. Rashin local gobernment autonomy:

Idan dai saboda al’umma zan yi, zan so ace nayi abun da ba’a taba yi a tarihin kankia ba musamman a matakin chairman. Amma idan aka ci gaba da joint account wannan ba zai yiwu ba saboda ba za’a samu wannan damar ba.

2. Tunanin siyasar ubangida ba ta chanchanta ba:Ba karamin gumurzu za ai ba cikin wannan kurarren lokacin samun takara daga jamiyyar mu. A yanayin yanda ake yin zaben local gobernment kuma akwai rudani idan ba ta nan ka fito ba sai dai kuma yin Mai duka.

3. Ba wasu matasa kwarin gwuiwa da kuma dama:Ina ba sauran matasan mu shawara da su yi anfani da damar wannan zaben su shiga siyasar domin taimakon alummar. Tabbas, ba karamin kuskure bane mu bar ta ga marasa kishin mu. Idan SIEC ba su yi hubbasa ba, tana yiwuwa INEC su bada damar damawa da kowa.

A karshe mu sani, kowa da komai yana wajen Allah kuma komai rubutacce ne kuma babu tabbatacce har abada.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *