September 17, 2026

Masu Adaidaita Sahu Za su Daidaita Sahu A Tafiyar Dakta Mustapha Inuwa A Katsina

0

Daga Aminu Salisu Tsagero

A cigaba da tuntuba da kungiyar Alheri Danko Ne karkashin jagorancin Alh Abubakar Ahmed Yantumaki sun sami ganawa da kungiyar masu KEKEN NAPEP domin tattauanawa da su dangane da wannan tafiya ta neman goyan bayan takarar Mustapha Inuwa shekarar 2023

Bayan an bude taro da addu’a Co-ordinator Alh Suleman Garba Kafinsoli ya gabatar Da jawabin maraba tare da yin godiya ga shuwagabannin wannan kungiya  ta masu Keke Napep a bisa wannan hadin kai da goyan baya da suke badawa acikin wannan tafiya ta sakataran gwamnatin Jihar Katsina.

Ana shi jawabin Darakta Janaral na wannan kungiya Alh Abubakar Ahmed ‘Yantumaki Ya bayyana makasudin kiran wannan taro inda yace sun kira wannan taro domin su zauna tare su tattauna su nemi alfarma da goyan baya da hadin kai akan wannan tafiya ta sakataran gwamnatin jihar Katsina Malam Mustapha Muhammad Inuwa.

Alh. Abubakar Ahmed Yantumaki ya kara da cewa wannan kungiyar ta masu KEKE NAPEP ma’ana ‘yar Kurkura tana da matukar mahimmancin gaske duba da kungiya ce mai dauke da shuwagabanni da mambobi  a fadin kananan hukumomi 34 da ke fadin jihar Katsina dan haka suke neman goyan baya.

Sai dai kuma a nashi bangaran shugaban wannan kungiya ta masu Keke Napep Alh. Jamilu Isiyaku katsina ya fara da yin godiya a bisa wannan karamci da shuwagabannin wannan kungiya ta “Alheri Danko Ne” suke yi masu tun kafin a gudanar da wannan zama wanda yake gudana.

Ya kara da cea a shire suke su bada hadin kai da goyan baya acikin wannan tafiya ta sakataran gwamnatin jihar Katsina domin wannan Itace kungiya ta farko a fadin jihar Katsina wanda ta fara tuntubarsu akan hidima irin ta siyasa adaidai wannan lokaci.

“Gaskiya na jidadin wannan kira da wannan kungiya ta  Alheri Danko Ne suka yi mana domin ina da tabbaci da yakinin cewa wannan tafiya ta mai girma sakataran gwamnatin jihar Katsina tafiya ce mai matukar mahimmancin gaske duba da irin gudunmuwar da ya bada a irin mukaman da ya rike anan jihar Katsina, dan haka al’ummar jihar Katsina suke yi mashi kyakkyawan zato idan Allah Madaukakin Sarki ya bashi wannan kujera ta gwamnan jihar Katsina za’a kara samun gaggarimin cigaba anan jihar Katsina.” Inji shi

Daga karshe kuma ya ce a shire suke su bada duk wata gudunmuwa da ake bukata domin ganin an samu nasara da ake nema idan kuma Allah madaukakin Sarki ya sanya an samu nasarar wannan al’amari to a tuna da irin gudunmuwar da kowa ya bada domin a taimakama mashi.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *