September 18, 2026

Gwamna Masari Yana Cikin Tsaka Mai Wuya A Zaɓukan Ƙananan Hukumomin Jihar Katsina…

0

Daga Mohammed Aminu Kabir

Shin anya za’a Iya yin Sahihin Zaɓe kamar Yadda gwamna yake So ?

Gwamna Masari ya sha nanatawa cewa baya da dan takara a zaɓuka masu zuwa kazalika bayada Wanda zai gajeshi a zaɓen Dubu Biyu da Ashirin da Ukku.

Koda yake manazarta na ganin cewa wannan zance ne kawai na Ƴan Siyasa, babu wanda zaice baya da wanda zai gajeshi bayan ya kammala Wa’adin mulkin shi.

Zaɓukan fitar da gwani na shuwagabannin ƙananan hukumomin jam’iyyar APC ya nuna cewa lallai kamar gwamnan baya da dan takara, tunda ya bada dama cewa aje a jaraba sasanci ko kuma ayi zaɓe Inda ba’a samu fahimatar juna ba wanda kuma haka akayi kuma kusan kowa ya gamsu da wannan tsarin a jam’iyyar ta APC.

Sai dai hausawa sukace bayan tiya akwai wata caca, akwai da yawa kuma da suke ganin sun marawa gwamnan baya a lokacin da yake neman jama’a amma yanzu su kuma suna son kawo nasu ‘yan takarar amma gwamnan yace Aaa aje dai ayi sasanci ko zaɓe.

Bisa dogon nazari akan rubutun da Hon. Abdullahi I. Mahuta yayi a jiya wanda yake nuni da cewa anyi ma wasu mutane dan baka zata ba wajen zaɓen fidda gwani na jamiyyar APC a faɗin jihar Katsina lallai akwai sauran rina a kaba.

La’akari da yadda aka gudanar da zaɓukan fidda gwani na shuwagabannin ƙananan hukumomin jihar Katsina a jam’iyyar APC da za’a yi zaɓen su nan bada jimawa ba, ya nuna cewa da dama da suke ganin cewa suna kusa da gwamnan basu samu yadda suke so ba kuma basu ji daɗin abinda ya faru ba dan haka dole zasu nemi hanyar da zasu rama.

Abinda ba za’a Iya sani ba shine ta wace hanya irin waɗannan Mutanen zasu iya rama wancen laifin da akayi masu ?

Alamu na nuna cewa akwai yiyuwar a iya yunƙurin sauya sunayen wasu ‘yan takara kafin zaɓen game gari wanda yin hakan kuma tabbas zai hasala wanda aka fidda sunan shi da magoya bayan shi, hakan kuma zai ƙara kawo rikicin cikin gida a jam’iyyar.

Yanzu zamu Iya cewa hwamna yana tsaka mai wuya kodai ya amince ayi zaɓe mai sahihanci ya rubuta sunan shi da ruwan gwal ko kuma ya amince da wutar da wasu zasu huro mashi ta biyan buƙatun su.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *