September 18, 2026

Manna Fastocin ‘Yan Siyasa A Gine-Ginen Gwamnati Laifi Ne Da Zai Iya Kai Mutun Gaba Kuliya Manta Sabo -Masari

0

Daga Katsina Post

Gwamna Masari ya hana lika fastocin ‘yan siyasa a rawul da gine-ginen gwamnati a Katsina

Gwamnan jihar Katsina, Rt Hon Aminu Bello Masari, CFR ya sa hannu a dokar tabbatar da tsaro mai lamba ta 5 wadda ta haramta duk wani nau’i na bangar siyasa da makamancin haka.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai dauke da sa hannun Kwamishinan yada labarai na jihar Katsina, Alhaji Abdulkarim Yahaya Sirika.

kamar yadda Katsina Post ta samu, na a karkashin damar da Gwamnan take da ita a karkashin sashe na 176 (2) na kundin dokar kasa ta shekarar 1999 da aka yiwa gyara da kuma ikon da Gwamnan yake da shi a karkashin duk wata doka data bashi dama.

Dokar Haramta aikata bangar siyasa da sauran laifuffukan da suka shafi haka ta fara aiki ne tun daga ranar 15th ga wannan watan na Fabreru, ta had da haramta sanya hotunan fastocin ‘yan takara na siyasa ko tutar nuna alama barkatai a bisa rawul da gine ginen gwamnati da ofisoshi da dukkan wasu guraren gwamnati.

Hakanan kuma dokar ta haramta taruwar gungun ‘yan bangar siyasar da aka fi sani da suna ‘Bacha’ ko ‘kauraye’ ko kuma duk wani suna da ake kiransu da niyyar cin mutumcin wani ko gungun jama’a.

Sanarwar ta cigaba da cewa “Duk wani ko gungun mutane da aka kama da aikata haka ta hanyar karya wannan dokar to za’a iya gurfanar dashi a karkashin tanadin hukuncin dokar a karkashin sashe na 114 na dokokin hukunta masu laifi na penal code

Gwamna Masari Ya Hana Lika Fastocin ‘yan Siyasa A Rawul Da Gine-ginen Gwamnati A Katsina

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *