EFCC Ta Ja Kunnen Yan Najeriya Su Daina Sayar Da Kuru’u.
Hukumar dake bankado masu yima tattalin arzukin Najeriya zagon kasa ta ja kunnen yan kasa dasu daina saye ko saida kuri’arsu a lokacin zabe.
Sakataren hukumar Dr. George Epungu ya yi wannan kiran jim kadan da amsar wata tawagar kungiyoyin fararen hula masu fafutukar yi ma zabe garanbawul a lokacin da suka kai ma hukumar ziyarar ban girma a Abuja.
Sakataren hukumar ya yaba ma kungiyoyin bisa zuwa su mika bukatarsu ta neman yin hadin gwiwa da hukumar don ganin an shawo kan matsalar ta saye da sayar da kuru’u a cikin kasar nan.
Shugaban tawagar Anyodare Atoye ya ce sun zo ne don yin hadin gwiwa da hukumar a magance wannan matsalar dake faruwa a lokacin zabe.
