Yan Gwangwani Ne Suka Fasa Tukunyar Data Illata Mutane 200 A Kano –NEMA.
Kimanin al’ummar Sharada dake cikin jihar Kano 200 ne aka kwantar da su asibiti a wannan Juma’ar data gabata bayan da suka shaki wani sinadari dake cikin wata tukunya da wasu yan gwangwani suka fasa.
Jami’in hukumar bada agajin gaggawa na kasa a jihar Kanon Dr. Nuraddeen Abdullahi ya tabbatar da hakan ga manema labarai a jihar.
Kamar yadda ya bayyana, yan gwangwanin sun fasa tukunyar ne da yammacin wannan Juma’ar a wata masana’anta dake Sharada.
Ya ce sinadarin ya galabaitar da mutanen da suka shake shi, tare da fidda su daga cikin hayyacinsu.
Babban daraktan kula da lafiya na asibitin Murtala dake Kano Dr. Hussaini Muhammad ya ce an kawo masu mutane sama da 75 da lamarin ya rutsa da su, kuma 65 yanzu haka sun samu sauki.
A wani labarin kuma ministar jin kai ta Najeriya Sa’adiyya Umar Faruq ta ziyarci wadanda lamarin ya rutsa da su a asibitin dake cikin garin Kano.
Ministar dai ta samu wakilcin babban daraktan ma’aikatar Dr. Nasir Sani Gwarzo.
Kuma yan jarida sun bada rohotan cewa, hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya, da takwararta ta Red Cross, da hukumar bada gajin gaggawa ta jihar Kano, suna cikin wadanda suka yi aikin ceto a lokacin da lamarin ya faru.
