September 18, 2026

Karamar Hukumar Batagarawa Ta Kafa Kwamitin Tara Kudaden Shiga.

0

Karamar hukumar Batagarawa ta kafa wani babban kwamiti akan tara kudin shiga a yankin.

Shugaban karamar hukumar Bala Garba Tsanni ne ya kaddamar da kwamitin a dakin taron karamar hukumar.

Ya ce an zabo membobin kwamitin ne duba da sahihancinsu domin a inganta kudaden da karamar hukumar ke samu.

Da yake maida jawabi, shugaban kwamitin Idris Gambo ya bada tabbacin yin aiki bisa gaskiya don inganta kudin shigar da karamar hukumar ke samu.

Ya ce kwamitin zai kuma lalubo wasu karin hanyoyin kudin shigar ga karamar hukumar ta Batagarawa.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *