September 19, 2026

‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Kaduna.

0

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 14 a karamar hukumar Kajuru ta jihar da safiyar yau Asabar.

Da yake tabbatar da hakan ga majiyarmu ta jaridar Sun, shugaban kula da harkokin kudi dana mulki na karamar hukumar Kajuru, Bala Jonathan ya bayyana sunayen wadanda aka sacen da suka hada da Abdullahi, Yakubu Isah, Samson Julius, Angelina Julius, Pasema Daniel, Junior Julius.

Sauran sun hada da Bobo Julius, Saratu Mohammed, Asenath Sunday, Confidence Jerry, Barnaki Sunday, Moses Kenneth, Danladi Goma da Ummi Jibrin.

“Wadannan su ne sunayen mutanen da aka sace a tashar Iri da aka gano a yanzu. Kuma lamarin ya faru ne da sanyin safiyar yau Asabar, 4 ga Yuni, 2022,” in ji Jonathan.

A cewar shugaban, har yanzu wasu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a baya suna cen hannun yanta’addan saboda ‘yan uwansu ba su samu damar hada kudin fansar amso su ba.

Batun garkuwa da mutane dai ya zama ruwan dare a unguwar Idon da ke Kajuru da kewayenta, wanda kuma ya janyo wa al’ummar da abin ya shafa shiga cikin halin kaka-nika-yi, hakan da ya sa suka rabu da dukiyoyin da gonakansu don amso yan uwansu daga hannun masu garkuwa da su.

Bayanan da aka samu sun nuna cewa, ‘yan bindigar sun rika kai munanan hare-hare a kan al’umomin dake kusa da Ungwar Makeri ta Mokoro Zankariya, unguwar Idon ward a Kajuru ba tare da wani martani daga gwamnatin jihar da jami’an tsaro na tabbatar da tsaro da rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin ba.

A cikin wannan shekarar kadai, an yi garkuwa da daruruwan mutanen yankin a Ungwan Makeri, garin Idon, Idon Hanyi, Agunu Dutse, Sabon Gari Kufana a cikin Kajuru da dai sauran su a kananan hukumomin Kajuru da Kachia dake makwabtaka da su.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *