Anyi Kira Gwamnatin Tarayyar Da Ta Janye Tallafin Mai Ta Maida Shii Ga Noma -Abdullahi Nakwanda
Daga Hussaini Ibrahim, Gusau
Shugaban kungiyar masu Noman masara na jihar, Zamfara, watau (MAN) Alhaji Abdullahi Kwanda, yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta cire tallafin man Fetir ta maida shi ga sashen Noma musamman takin ɗan tallafin abinci yafi mahimmanci akan na man Fetir.
Abdullahi Kwanda ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke tattaunawa da wakilin mu a Gusau babban birnin jihar Zamfara.
Nakwada ya ƙara da cewa, bilyoyin nairori da gwamnati ke badawa wajan ɗauko man fetir da gwamnati zata bada su wajan takin zamani lallai da munciyar da Afrika baki ɗaya arzikin ƙasar mu zai bunƙasa fiye da yadda bamuyi tsammani. dan taki zai wadata manoma zasu samu taki cikin farashi mai sauki, matasa zasu samu abin yi rani da damuna.
kuma zai rage zaman kashe wando ga matasa kuma zaitaimaka wajan samar da tsaro, haka kuma aikin gona rigakafine ga matasa wajan dogara dakai.
Kazalika zai samar da ingantacan danwamaman zaman lafiya dan idan matasan mu basu da aikin yi, abu mai saukine su faɗa a harkar da bata dace da su ba. Inji Shugaban manoman masara na jihar Zamfara.
Ya ya koma kan batun manyan ‘yan kasuwa kuma masu sana’ar saida taki shugaban yayi kira a garesu da su samar da kamfanoni sarafa taki a cikin wannan gida ƙasa tamu ta yadda babu bukatar sayan takin zamani na qasashen wake.
A cewarsa yanzu haka akwai Kamfanin da ke yin takin zamani mai inganci a ƙasar nan wanda ƙananan manoma zasu yi amfani da shi kuma su samu amfanin mai inganci.
Haka kazalikama idan gwamnatin jihohi masu kamfanin taki zasu tada kamfanonin su zasu iya samar da taki ga manoma da za suyi amfani da shi acikin sassaukan farashi a samar da abincin da ba’ayi tsamaniba.
A ƙarshe Abdullahi Kwanda yayi kira musamman ga manoman masara da kada tsadar taki ta basu tsoro a noman bana ya kamata suyi amfani da takin gargajiya da kuma takin da ake yin sa anan ƙasar mai saukin farashi kuma yana da Inganci sosai wajan gudanar na noman su.
Ya ƙara da cewa dan yanzu haka akwai shiri na musamman da uwar kungiyar ta masu noman Masara keyi, ƙarƙashin jagoranci Shugaban ta na Kasa, Alhaji Bello Annur, dan samarwa mambobin kungiyar hanyoyin cigaban noma na zamani.
