September 17, 2026

Wani Abu Ya Sake Fashewa A Jihar Kogi.

0

Hakan dai na zuwa ne kwanaki 18 da fashewar wani abu a yankin na Kabba dake jihar Kogi.

Fashe na baya-bayan nan da ake kyautata zaton ya faru ne a daren Lahadin da ta gabata a wani dakin shan barasa da ke Okepadi, lokacin da magoya bayan jam’iyyar PDP ke daf da gudanar da bukukuwan murnar fitowar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

Jaridar LEADERSHIP ta ce, Fashewar farko wacce ta biyo bayan cece-kuce kan ko bam ne ko kuma iskar gas, ta faru ne a ranar 11 ga Mayu, 2022, kuma a wani wurin shan giya kusa da Junction Lewu a cikin garin.

Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi kwanaki 18 da fashewar na farko, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, William Aya, ya ce fashewar ta faru ne a wata mashaya ta Omofemi dake Okepadi Quarters, Kabba, da misalin karfe 9:15 na yammacin Lahadi.

Ya ce kawo yanzu ba a samu asarar rai ba, amma ana bincike kan lamarin domin bankado gaskiyar labari dake tattare da fashewar abun.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *