Yan Sanda Sun Harbi Dan Jarida Da Wasu 2 Yayin Zanga-Zanga A Osun.
Wani dan sanda ya harbi wakilin jaridar The Nation mai suna Toba Adedeji a Olaiya dake Osogbo, babban birnin jihar Osun, yayin wata zanga-zangar da wasu fusatattun matasa suka yi.
An harbe shi ne a kafarsa ta hagu, yayin da wasu mutane akalla biyu kuma aka harbe su suma.
Wasu fusatattun matasa dai ne suka taru a mahadar wurin domin nuna rashin jin dadinsu da kisan abokin aikinsu, Abiola Afolabi.
Afolabi, wanda aka ce an binne shi a wata makabarta a garin Ilesa na jihar, an harbe shi ne bisa zarginsa da laifin damfara ta intanet.
Jami’an ‘yan sandan dauke da makamai sun isa wurin da zanga-zangar, inda suka fara harbi, inda a kan haka ne suka samu wani dan jaridan a yayin da yake gudanar da aikinsa, inji jaridar LEADERSHIP.
An kuma garzaya da Adedeji zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Osun (OSUTH) dake Ogbobo.
