September 16, 2026

Yan Ta’adda Sun Sace Dalibai, Tare Da Kona Motocinsu A Kaduna.

0

Wasu ‘yan bindiga a wannan Talatar sun sace dalibai da matafiya a kan babbar hanyar Birnin Gwari, a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

An bada rohotan cewa, ‘yan bindigar sun kuma kona motoci takwas da daliban ke ciki don tafiya rubuta jarabawar shiga makarantar koyon fasahar kiwon lafiya da ke Makarfi, wadda aka shirya gudanarwa a jami’ar Jihar Kaduna.

Jami’in hulda da jama’a na kungiyar masu ci gaban masarautar Birnin Gwari, Idris Sa’idu, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce ‘yan bindigar sun killace wurare uku daban-daban a kan babbar hanyar, inda suka tilastawa masu ababen hawa juyawa

A cewar kakakin, wadanda ba su yi sa’ar fada ma tarkon da ‘yan ta’addan suka dana bane, aka yi awan gaba da su daga bisani.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “An sace dimbin matafiya da daliban da za su rubuta jarrabawar shiga Makarantar Lafiya ta Makarfi mai alaka da Jami’ar Jihar Kaduna, inji jaridar PUNCH.

“Daya daga cikin jami’an mu Abubakar Haruna Babajo da ya samu sa’ar tserewa, ya ce ‘yan bindigar sun kona motoci 8 bayan sun yi awon gaba da fasinjojin.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *