Dan Takarar Gwamnan Bauchi A PDP Ya Janye.
Jam’iyyar PDP a jihar Bauchi na shirin gudanar da sabon zaben fidda gwani na gwamna bayan da dan takarar gwamna na jam’iyyar, Kassim Ibrahim Mohammed ya janye.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilin jaridar LEADERSHIP a wannan Talatar, sakataren yada labarai na jam’iyyar a jihar Alhaji Yayanuwa Zainabari ya bayyana cewa dan takarar gwamnan na jam’iyyar PDP bisa radin kansa ya janye daga takarar gwamna a 2023.
A cewar Zainbari, za a gudanar da sabon zaben fidda gwani a ranar Asabar.
Idan dai ba a manta ba, Mohammed shi ne dan takarar gwamna daya tilo a zaben fidda gwani na jam’iyyar, inda ya tara dukkan kuri’un wakilai 655 baya ga daya da ta yi dameji, wanda hakan ya bashi damar zama dan takarar gwamna a makon jiya.
Mohammed, wanda shi ne tsohon sakataren gwamnatin jihar, ya shiga takarar gwamnan Bauchi ne bayan gwamna mai ci Bala Mohammed ya zabi takarar shugaban kasa a jam’iyyar.
Sai dai Gwamna Mohammed ya sha kaye a zaben fidda gwani na shugaban kasa da aka gudanar a Abuja a karshen makon da ya gabata.
