Aminu Nuhu Abdulkadir Ya Zama Kauran Katsina
mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya amince da nadin Alhaji Aminu Nuhu Abdulkadir a matsayin Sabon Kauran Katsina Hakimin Rimi
Wannan nadi na zuwa ne bayan da Allah ya yi wa Kauran Katsina Hakimin Rimi Alhaji Nuhu Abdulkadir rasuwa kwanakin baya.
Aminu Nuhu Abdulkadir wanda aka fi sani Ciroman Kaura ko wakilin Kaura ya ga ji mahaifinsa, sakamakon wannan nadi da mai martaba sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya yi masa.
Muna taya shi addu’a Allah ya bashi ikon sauke wannan nauyi da ya rataya akan sa.
