September 17, 2026

Ma’aikatar Kasafi Ta Yi Karin haske Kan Kasafin Jihar Yobe Na 2023

0

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

Kwamishina a Ma’aikatar Kasafin Kudi da tsare-tsaren tattalin arziki a jihar Yobe, Mohammed Garba Gagiyo, ranar Alhamis, a tattaunawar da ya yi da manema labaru, a ofishin sa dake Damaturu, ya yi karin haske dangane da yadda kudurin kasafin 2023, wanda Gwamnan jihar, Hon. Mai Mala Buni ya gabatar wa majalisar dokokin jihar.

Mohammed Gagiyo ya ce, gwamnatin ta ware N87,800,717,000, kimanin kaso 53.8 bisa dari a Kasafin domin ayyukan yau da kullum, yayin da aka ware N75,354,649,00, daidai da kashi 46.2 cikin dari domin gudanar da manyan ayyuka.

Har wala yau kuma, Kwamishinan ya bayyana hanyoyin da za a yi amfani dasu wajen samar da kudaden kudurin kasafin kudin 2023, sun hada daga asusun ajiya na kimanin N8,500,000, 000, kudaden shiga na cikin gida wadanda ake sa ran samu kimanin N12,251,677,000 tare da na asusun hadaka na tarayya (Statutory Allocation) N38,555,341,000.

Ya ce sauran sun hada da harajin N25,793,593,000, asusun gwamnatin tarayya, N4,654,755,000 da kason jihar na kudaden zuba jari, N73,400,000,000 wanda jimlar kudin ya kai N163,155,366,000.

Hon. Muhammad Gagiyo ya ce a cikin kasafin 2023 wanda aka gabatar, an warewa Ma’aikatar kasuwanci, masana’antu da yawon bude ido Naira biliyan 4.460, Ma’aikatar ayyuka Naira biliyan 8.944, Ma’aikatar Ilimi a matakin farko Naira 4.997, ta Noma Naira biliyan 4.551.

Kwamishinan ya ce sauran sun hada da hukumar samar da wutar lantarki da raya yankunan karkara, naira biliyan 3.5, ma’aikatar lafiya naira biliyan 3.479, Ma’aikatar bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi, naira biliyan 1.5, sai Ma’aikatar ayyukan jin kai, naira miliyan 950, sai ofishin Sakataren Gwamnatin jihar Yobe, Naira Biliyan 1.523 da Ma’aikatar Watsa Labarai Naira Miliyan 280.

Bugu da kari kuma, Hon. Gagiyo ya yaba wa Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, bisa kokarin da yake yi na ganin jihar ta bunkasa, duk da matsalolin koma bayan tattalin arziki da Nijeriya ke fuskanta, ya jaddada cewa idan aka samu nasarar aiwatar da kasafin kudin shekarar 2023, zai kai jihar ga wani mataki na ci gaba.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *