FUDMA Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Mashawarta Akan Cibiyar Alkur’ani Da Bincike
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Jami’ar Gwamnatin Tarayyar da ke Dutsima (FUDMA) ta ƙaddamar da kwamitin mutane 13 karkashin jagorancin baban mai shari’a, Musa Ɗanladi Abubakar da zai riƙa bada shawara akan yadda za a inganta cibiyar bincike da bunƙasa karatun Alkur’ani mai girma a jami’ar.
Da yake jawabi a wajan ƙaddamar da wannan kwamiti mataimakin shugaban jami’ar FUDMA Farfesa Armaya’u Bichi ya ce an zaɓop
waɗanda aka naɗa bisa la’akari da cancantar su.
Ya ƙara da cewa mutanen sun samu nasarori a wasu ayyuka da suka yi acikin al’ummar su, da sadaukar da kansu wajan ciyar da addinin musulunci gaba.
Farfesa Bichi wanda mataimakin sa Dakta Aminu Ado ya wakilta ya ce FUDMA a matsayin ta na jami’a ta himmatu wajan laluɓo hanyoyin cigaba da na dan adam musamman neman ilimi.
Ya kuma bada tabbacin bada duk wata gudunmawa domin samun sakamakon da ake buƙata wajan tafiyar da sha’anin wannan cibiya ta bincike da kuma karatun Alkur’ani mai girma.
Da yake mayar da martani a madadin waɗanda aka naɗa, shugaban kwamitin kuma baban alkalin jihar Katsina, Mai Shari’a Musa Ɗanladi ya gode wa shugabannin jami’ar da suka yi aiki tukuru wajan zaɓen waɗanda suka cancanci naɗin kuma ya yi alƙawarin yin amfani da dimbin ilimin da suka samu wajen bayar da gudummawa ga ci gaban manufofin cibiyar.
A cewar sa, dukkanin masu ruwa da tsaki za su taka rawar gani wajen tabbatar da ganin yara sun koma makaranta don samun kyakkyawar makoma da al’umma gaba ɗaya “suna cewa ganin yara suna yawo a tituna a lokutan makaranta alama ce ta gazawar mu kuma dole ne mu tashi mu yi abin da ya dace tare” inji shi
Mambobin kwamitin sun haɗa da; da Farfesa. Adamu Abubakar Gwarzo, Shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN), a matsayin Mataimakin Shugaban Jami’ar; Farfesa. Ibrahim Muhammad da ‘Yanɗakan Katsina Hakimin Dutsima Alhaji Sada Muhammad Sada da Alh. Abubakar Jalli Gambo da kuma Alh. Aminu Makera.
Sauran su ne Sheikh Gwani Abubakar Said Musa (Funtua) da Shiek Yakubu Musa Hassan Katsina da Ambasada Isa Dodo da Gwani Muhammad Adam Alkali oon da Garkuwan Gwanayen Alkurni da Alh. Iro Maikano Fagachin Katsina Hakimin da Matazu.
Alh. Bilya Sanda, Khadimul Islam shi ne matsayin daraktan cibiyar ya yin da dakta Jabir Musa Suleiman zai yi aiki a matsayin Sakatare
