November 18, 2026

Abubuwa 10 Da Za a Riƙa Tunawa Da Hon. Salisu Iro Isansi Da Su A Siyasar Ƙaramar Hukumar Katsina. (2)

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Cigaba daga rubutun farko

  1. SADAUKARWA: Duk tsawon lokaci da aka ɗauka Hon. Salisu yana majalisar tarayya ya sadaukar da komi na shi domin al’ummar da yake wakilta waɗanda suka zaɓe shi.

Idan aka ce wane mutum ne mai sadaukarwa to hakan na nufin a kowane irin al’amari na shi, ba wai na siyasa ba, muna iya ganin cewa Hon. Salisu Iro Isansi ya siffanta da wannan aiki da kuma kalma a matsayin sa na wakili.

Wannan batu na sadaukarwa ya yi hannun riga ga sauran ‘yan siyasar Katsina ta tsakiya waɗanda ake bada misalin su da mutane masu san rai, shi kuwa gogan namu sai dai wancan
n kalma, idan wani ya isa ya yi abinda Hon. Salisu ya y har ya samu wannan laƙani mana.

Yanzu haka abinda masana ke cewa shi ne, tunda ƙaramar hukumar Katsina ta yi baban rashin sadauki kuma jagora mai aiki da ilimi da basira wajan wakilcin jama’a, akwai tsoro na hannun wa kuma Katsina ta tsakiya zata faɗa.?

  1. TAWAKALI: Yana da wahalar gaske ace mutum yana da tawakali kuma bai samu nasara a rayuwarsa ba, Hon. Salisu Iro Isansi ya cinye jarabawar da ya fuskanta ta hanyar yin tawakali da maida al’amari ga Allah.

Daga yanzu duk wata nasara da Hon. Salisu Iro Isansi zai samu a rayuwa dole tana alaƙa da tawakali da maida al’amari ga Allah da ya yi, daman an ce ba a gane mumini na kirki sai wata jarabawa ta same shi.

Bisa dukkan alamu za a yi mamakin wasu nasarori da za su zo wa Hon. Salisu Iro Isansi wanda sai jama’a sun rika tuhumar yadda aka yi idan ba sun tuna da halin da ya shiga ba kuma ya yi tawakali, wannan wani ɓangare ne na rayuwa da Allah ke ba bawansa a lokacin da ya so.

Nan gaba duk mai son yin nasara a siyasar Ƙaramar Hukumar Katsina dole Hon. Salisu Isansi ya kasance madubi da za a riƙa tunawa da shi kuma zai zama abin koyi a Rayuwa, idan da zan samu dama zai rubuta littafi akan shi don al’umma masu son kafa tarihi a siyasa su riƙa amfani da shi wajan samun nasara a rayuwa.

  1. JAGORA: Hon. Salisu Iro Isansi jagora ne a siyasa, bakina da goro da na baku labarin irin faɗi tashi da gwagwarmaya da ya sha kafin zuwa wannan lokaci, ya kasance mutum guda ɗaya da mutum fiye da dubu suka sanya gaba suna neman ganin bayansa, amana cikin ikon mai sama, gashi nan ya zama madubin siyasar Katsina, haka Allah ya so kuma haka ake yi.

Kasancewar jagora a tafiyar siyasar Katsina ta tsakiya yana cigaba da samun gudunmawa daga wasu masu kishi, da san cigaban al’umma wajan samun ƙarfin hali da jan ragamar duk wanda ke tare da shi, da kuma ba su hakuri na ɗauke zafin dafin abinda ya dame shi a siyasa.

Kodayake faɗuwar gwarzo nasara ce, babu ɗan siyasar da yasan abinda yake da bai tausaya wa Hon. Salisu ba, wannan ma kaɗai nasara a a siyasa, duk maganar da zaka ji anyi akan sa fatan alheri ce da kyautata zato, da su wane sun samu wannan sun ji ƙamshin nasara a siyasa

Jagora ke nan, duk bala’in da aka rika shirya masa, yana ji kuma yana gani, sannan yasan daga inda wutar take, amma bai taɓa tankawa ba ko nuna damuwa balanta ya yi korafi, hatta masoyansa ya hana su nuna damuwa da korafi duk al’ummar da ta rasa mutum irin wannan to ayi mata jaje, Katsina ta tsakiya Allah ya tsayar nan.

  1. KYAUTA: Hon. Salisu ya kasance mutum mai kyauta amma kuma baya son ana faɗa domin ya ce shi yana yi ne domin Allah saboda haka duk wanda Allah yasa yana da rabo kuma suka haɗu da shi haduwa ta mutunci to mutum shi zai bada bayani.

Daman can Allah ya yi shi mutum ne da yasan mutunci da darajar wanda yake tare da su, yana da wahala ka ji wani kusa da shi yana kuka da halayyar Hon. Salisu Iro Isansi musamman wajan cika alƙawari idan ya ɗauka.

Hon. Salisu ya kware wajan faɗawa mutum gaskiya musamman idan ka zo mashi da buƙata, shi yasa wasu ke yi masa kallon kamar bako a siyasa saboda ya kasa koyon shirya karya irin su wane balantana kuma ɗaukar alƙawarin da ba a iya cikawa, kai wannan abu da ciwo yake, ina ma a ce su wane da wane za su yi koyi da Hon. Isansi da sun huta.

Kyauta dai halinka ce, kuma nasan ba zaka fasa yi ba, tunda baka fara don ka daina ba, idan sauran jama’a sun ga dama su yi koyi da kai kana da lada, idan kuma aka tuna da kai zaka samu yabo da Addu’o’i a siyasar ƙaramar hukumar Katsina ta tsakiya, to don Allah me ya fi wannan?

  1. KAMMALAWA: Kaɗan daga cikin abubuwan 10 ke nan waɗanda duk lokacin da aka yi batun su a siyasar ƙaramar hukumar Katsina to Hon. Salisu Iro Isansi zai zo maku a rai da tunawa da shi da jajan tawa juna saboda rashin shi.

Na yi imanin cewa, ya ciri tuta a siyasar ya nuna halin Dattaku da yakana ya zama mutum na daban bai kwafsa ba, bai bata tarihin sa ba, amma ya kafa sabon tarihi, komin tsawon lokaci sai an tuna da shi.

Ga ka dai ƙarami mai ƙananan shekaru a siyasa amma kuma yana da halin manya da suka yi siyasa suka gama lafiya kuma za a cigaba da tunawa da su duk lokacin da ‘yan sari suka kwafsa a siyasar ƙaramar hukumar Katsina.

insha’Allahu anan nake bankwana da masu karatu, ina godiya da kuka ɓata lokaci wajan karanta wannan rubutu nawa. Sannan ina yi maku albashi da sabon rubutu na Mai taken Hon. Salisu Iro Isansi Ɗaya Bayan Ɗaya. Na gode.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *