Karamar hukumar Zango ta dauki matakan dakile yawan hadurra.
Karamar hukumar Zango dake cikin jihar Katsina ta dauki matakan dakile yawan hadurra da kuma karya doka da ake yawan yi a yakin.
Hakan dai ya biyo bayan wani taro da aka gudanar tsakani shugaban karamar hukumar da kuma masu ruwa da tsaki da abun yashafa domin lalubo hanyar magance matsalolin, inji jaridar Popular News Hausa.
Taron wanda ya samu halartar jami’an hukumar kiyaye hadurra ta kasa, yan sanda, jami’an hukumar kula dashige da ficen Najeriya, jami’an tsaron farin kaya, sarakunan gargajiya, alkalai da sauran jami’ai daga jamhuriyar Nijar, ya tattauna hanyoyin da za a magance matsalar a fadin karamar hukumar.
Shugaban karamar hukumar Babangida Ali Yardaje ya bayyana damuwar sa kan yadda karuwar hadurra da masu motoci da mashina ke haddasawa musamman masu zuwa daga jamhuriyar Niger ke zama matsala.
Alhaji Babangida Yardaje wanda ya koka kan yadda hadarru ke haddasa munanan raunuka da rasa rayukan al’umma da dama a yankin, ya tabbatar ta cewa karamar hukumar ba zata sa ido hakan ya ci gaba da faruwa ba.
Daga nan sai shugaban karamar hukumar ya jawo hankalin jami’an tsaro dake aiki a yankin da su gurfanar da dukkan wanda aka kama ya karya doka gaban kuliya manta sabo.
Haka zalika Alhaji Babangida Ali Yardaje ya jawo hankalin mahukunta jamhuriyar Niger da su fadakar da al’ummar su akan matsalar dake tattare da tukin ganganci.
A jawabin sa kwamandan hukumar kiyaye haddura mai kula da shiyyar Daura ACD Yakubu Maina ya gode ma shugaban karamar hukumar bisa shirya taron, tare da bada tabbacin su na yin bakin kokarinsu domin rage afkuwar hadurran a yankin.
Shima ana shi jawabin wakilin Mulkan Daura hakimin Zango Alhaji Ubale Sani ya tabbatar da bada cikakken goyan bayan shi domin cimma abinda aka sa gaba.
