NAPTIP Ta Ja Kunnen Yan Najeriya Da Su Guji Biye Ma Masu Yaudarar Su Da Sunan Samun Aikin Yi Zuwa Kkasashen Waje.
Hukumar yaki da safarar bil’adama ta Najeriya NAPTIP ta ja kunnen al’umma da su gaji biye wa masu yaudarar su da sunan samun ayyukan a kasashen waje.
Hukumar ta ce maimakon haka, sai su ƙare ga fadawa cikin abubuwan cin zarafi ta hanyar lalata.
Kwamandan hukumar ta jihar Anambra Mrs. Ibadin Judith Chukwu ta bayyana hakan ga manema labarai a Akwa wurin bikin tunawa da ranar yaki da safarar bil’adama.
Ta bayyana cewa, masu yin safarar mutanen sun fi san matasa don saka su cikin harkar lalata a kasashen dake yankin Asia.
Mrs. Judith ta ce munin safarar bil’adama na karuwa saboda zuwan fasahar sadarwar zamani, tare da bayyana damuwa duba yadda mafi yawancin mutanen da aka yi safarar su ke mutuwa kan hanya.
Da kwamandar hukumar ke maida martani akan taken bikin ranar mai suna “amfani da kuma rashin amfanin fasahar zamani”, ta yi bayani hanyoyi daban daban da masu safarar bil’adamar ke amfani fasahar zamani wurin yin wannan haramtaccen kasuwanci.
Ta bada misali da cewa suna tallata guraben ayyukan yi ta yanar gizo, inda kuma suke samun sa’ar nadar bayanan mutanen don saka su ciki.
