DAMBARWAR TSIGE MATAIMAKIN GWAMNAN ZAMFARA — Maiwada Dammallam
Da mamaki yadda majalisar Jihar Zamfara ta samu kawowa matakin Kusa da k’arshe na tsige Mataimakin Gwamna Jihar a inda yanzu maganar takai har gaban Alkalin-Alkalan Jihar inda nan za’a tabbatar da tuhume tuhumen da akeyi ma Mataimakin Gwamna, a kuma zartas mashi da hukunci..
Abin kula anan shine irin yadda doka ke aiki cikin hanzari Idan ta shafi biyan bukatun y’an siyasa fiye da idan matsalar al’umma ce ta gama-gari.
Yadda y’an ta’adda ke cin zarafin talaka, suna kashe na kashewa, su wulakanta na wulakantawa, kuma y’an sanda na kama wasu daga cikin masu aikata wannan mummunan abu, mutum sai ya dauka a Jihar Zamfara babu Majalisa, babu kotuna, babu Alkalai ballantana Alkalin-Alkalai duba da yadda babu dan ta’adda daya tak da Majalisa da Kotuna sukayi tsayin daka wajen ganin anyi ma hukunci daidai da bala’in da suka jefa Jihar a ciki.
Mutum zaifi yarda da hakan musamman Idan aka kalli rashin daukar mataki mai tsauri kan Sarakuna 5 da Hakimai 34 wadanda Kwamitin bincike da Jihar ta kafa don gano musabbabin annobar ya gano suna da hannu dumu-dumu cikin wanzar da bala.
Kenan, da mamaki Majalisar Dokoki ta Jihar da kasa tirsasa a hukunta wadannan azzaluman Shugabanni, ta tada kayar baya wajen ganin an tsige Mataimakin Gwamna dan kawai yaki chanza sheka tare da Gwamna lokacin da shi Gwamnan ya dawo jam’iyar APC.
Wannan shi ake cema hin karfi ga na gida. Nasan dai da yawa zasu yarda cewa wannan tsigewar bata da wata nasaba rayuwa ko walwalar talakan Zamfara sai siyasa da walwalar Gwamna da mukarraban shi.
Ina ma ace wannan jan idon da Majalisar Zamfara keyi, tana yi ne don gani Hukumomi sun kamo tare da hukunta manyan y’an ta’addar da suka addabi jihar; suke kashe talakawa kan kari tare da cin zarafin mata da kuma jefa yara cikin halin-ha’ulahi.
Tabbas da Mataimakin Gwamna yayi biyayya yabi Gwamna Jam’iyar APC da babu mai jin cewa yayi wandaka da kudade a ofishin shi ballantana har akai idan za’a yi tunanin tsige shi. Hakika akwai darasi ga talaka cikin wannan dambarwar. Biki na kuraye wanda akuya cikin gara take ba cikin y’an biki ba.
Idan Gwamna da Majalisa sun ce saboda Mataimakin Gwamna ya zalunci talakan Zamfara ta hanyar wandaka da kudin gwamnati shiyasa zasu cire shi, talakan da ya yarda shi yaso.
Haka-zalika, Idan Mataimakin Gwamna yace saboda yana son talaka ko don yana kare martabar shi za’a tsige shi, talakan da ya yarda shi yaso.
Abin fahimta anan shine, talaka bai da banbanci da kwallo a filin tamola — wannan ya buga, ya ba wanchan ya buga. Yana da muhimmanci talaka ya mike tsaye wajen fahimtar yadda wannan wasan yake, ya kuma gane matsayin shi na huhun-ma-ahu a wasan.
Duk talakan da zai tada jijiyar wuyan shi kan wannan matsalar, to yayi kokarin gane ribar yin hakan a gare shi don dai a bayyane yake cewa babu riba ga talakawa a dunkule.
Idan ma hayar mutum aka dauka don yayi fushi ko ya nuna bacin ranshi kan an “zalunci” wani bangare, to ya tabbata ya amshi farashi mai tsoka don ba kullum irin wannan damar ke gittawa ba.
Daga karshe, tambaya ga Honorabul Shamsudden Hassan Bosko, Shugaban Kwamitin Watsa Labarai na majalisar Zamfara, Ina aka tsaya maganar Sarakuna 5 da Hakimai 34 da bincike ya bankado suna da hannu a zaluncin da ake ma Zamfarawa, kuma Ina labarin Turji wanda ya hana kowa sakat a Jihar Zamfara?
