September 18, 2026

Hon. Ado Doguwa Ya Baiwa Tsangayar Sadarwa ta Jami’ar Bayero Tallafin Miliyan 10

0

Daga Salisu Hamisu Ali

Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya kuma dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Tudun Wada da Doguwa ya bada gudunmawar Naira Miliyan 10 ga tsangayar sadarwa ta jami’ar Bayero dake Kano.

Dan majalisar wanda tsohon dalibi ne a sashin koyar da aikin jarida na jami’ar Bayero ya bayyana bayar da gudunmawar ne a yau Asabar yayin taron cika shekaru 40 da yaye daliban farko na sashin koyar da aikin jarida dake Jami’ar.

Taron na kwana biyu wanda a ka kammala shi a yau Asabar ya samu halartar tsofaffin daliban sashin koyar da aikin jarida na jami’ar da suka hada; Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, shugaban kwamitin tsaro na majalisar wakilan Najeriya, Sha’aban Ibrahim Sharada da sauran manyan baki.

Tunda farko Alhassan Ado ya bayyana cewa suna matukar farin ciki da alfahari kasancewarsa daya daga cikin daliban da sashin koyar da aikin jarida ya yaye.

“Muna alfahari kasancewarmu wadanda wannan babbar jami’a ta yaye, sannan ina alfahari kasancewata daya daga cikin daliban sashin koyar da aikin jarida na wannan jami’a.

” Idan zan iya tunawa a lokacin da muka fara, idan muna muhawara da sauran daliban jami’o’i suna cewa jami’ar Ahmadu Bello ce kan gaba, wasu suce jami’ar Legas, amma ina alfahari da cewa sashin koyar da aikin jarida na jami’ar Bayero ya sha gaban kowanne a fadin tarayyar Najeriya.”

Shugaban masu rinjayen ya bayyana cewa a bisa abinda jami’ar ta bashi na ilimi yakamata ya yi wani abu na Alkhairi ga jami’ar.

“Dangane da abin da wannan sashi na koyar da aikin jarida ya bani a fannin ilimi da tarbiya, zan so sanar da bayar da tallafin kudi na Naira Miliyan 10, wanda za a raba shi ga sashin koyarwa na jami’ar Bayero da kuma tsangayar sadarwa gabadaya”.

Shi ma anasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya godewa Allah bisa ni’imar da yayiwa jami’ar sannan ya yi kira ga daliban da jami’ar ta yaye da su dinga tallafa mata.

Prime time Hausa

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *