Akwai Alamun Maryam Salisu (Sabuwar Jaruma) Zata Taka Rawar Gani A Shekarar 2026
DAGA MUKHTAR YAKUBU
Sabuwar Jaruma a masana’antar Kannywood Maryam Salisu ta fito shirin ta na zama babbar jarumar da kowa zai yi maraba da ita da zarar ta samu damar da za ta baje kolin basirar ta a cikin harkar ta Kannywood.
Babu shakka idan har Maryam Salisu ta samu damar da take so ta samu na ɗaurin gindi daga masu juya harkar masana’antar, to ba abin mamaki ba ne cikin ɗan kankanin lokaci ta kai ga matakin da kowa zai san da ita.
Ba don komai ba kuwa, sai don yadda Maryam Salisu ta kasance yarinya mai saukin kai da kuma girmama na gaba da ita sannan daidai gwargwado tana da ilimi da kuma tarbiyya.
Sannan duk wata siffa ta ƙyan sura da mata suke ji da ita, Maryam Salisu za a iya saka ta a cikin ƙyawawan mata.
A cikin wata tattaunawa da muka yi da ita, sabuwar Jarumar ta yi mana bayanin dalilin ta na shiga harkar fim, burin da take da shi da kuma sauran batutuwa da suka shafi rayuwar ta. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar tamu ta kasance.
Da farko za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatun mu.
Maryam Salisu: To Assalamu Alaikum da farko ni dai suna Maryam Salisu kuma an haifeni ne garin Jos a yanzu ina da shekara 23, na yi karatun firamare da sikandare duk a garin Jos. Bayan na kammala karatu da ɗan wani lokaci sai na dawo Kano a yanzu ina zaune a garin Kano, kuma ina aiki ko sana’a ta harkar gyaran jiki wanda a yanzu shi ne abinda na fi kwarewa da shi a matsayin sana’ar da nake yi.
Kina ɗaya daga cikin sabbin jarumai da suka shiga harkar fim a wannan lokacin, ko me ya ba ki sha’awar shiga harkar fim ɗin a wannan lokacin?
Maryam Salisu: To gaskiya daman ba a wannan lokacin ne na fara sha’awar na yi harkar fim ɗin ba. Ina da sha’awa ta shiga harkar tun ina ƙarama, amma da yake ina karatu , kuma ga ni karama a lokacin na san ko da na so na shi ba za a bar ni ba a gida. Don haka sai na bari zuwa lokacin da zan kammala karatun domin hakan zai fi mani sauki.
A yanzu da na kammala karatu kuma ga shi ina garin Kano da zama wadda ita ce cibiyar harkar fim ɗin, sai na ga ya kamata na gwada neman damar da zan cika burina na zama jaruma a cikin masana’antar Kannywood. Kuma a yanzu Alhamdulillah, ina ganin buƙatar da nake da ita za ta biya saboda alaƙar da nake ta samu da ‘yan fim da a kullum muke tare da su.
Duk lokacin da mace za ta shiga harkar fim ta na samun matsala a gida ko a cikin kawayen ta saboda za su rinƙa cewa saboda me za ta shiga harkar fim. Ko kin samu irin wannan ƙalubale daga gida ko kawaye?
Maryam Salisu: To gaskiya ni ban samu hakan ba, saboda ko a baya don ina karatu ne sai na ga a wannan lokacin iyayena ba za su bar ni ba, amma da na gama sikandare ban samu matsala ba, kuma ta ɓangaren kawaye ma ai wannan ba ta taso ba saboda kowa yana nemarwa kansa mafita ne tun da a yanzu na girma na mallaki hankali na ai ina da damar da zan gane abu mai kyau da wanda ba shi da kyau. A yanzu iyayena su ne za su ce na yi ko kada na yi, saboda a ƙarƙashin su nake, su kuma sun bani damar na yi, to ai ka ga ba ni da matsala.
A yanzu da kika shigo cikin ‘yan fim, ya kike ganin yadda suke rayuwa?
Maryam Salisu: Gaskiya na ga yadda suke rayuwar su tana burgeni, domin duk yadda ake maganar su da na haɗu da su sai na ga ba haka suke ba. Ana mu’amala ta mutunci ga girmama juna, da yawa da na haɗu da su sun nuna mani kauna, don haka suna da kirki da kaunar junan su
Baya ga harkar gyaran jiki ko akwai wani abu da kika fi kwarewa?
Maryam Salisu: Eh, ina da kwarewa a harkar tallace tallace wanda nake yi wa kamfanoni kuma gaskiya na kware sosai, domin muna yi wa kamfanoni da dama talla, kuma a yanzu ina kan yi duk wani kamfani da yake son na yi masa talla na kayan sa kofa a buɗe take a wajena.
Harkar fim a wajen ki sha’awa ce ko kuma wani buri kike so ki cika?
Maryam Salisu: Gaskiya harkar fim a wajena ta fi karfin sha’awa, domin zan yi fim ne a matsayin sana’a wadda zan yi amfani da ita wajen rufawa kaina asiri tare da kiyaye mutunci na, domin a yanzu sana’ar ka mutuncin ka don haka harkar fim sana’a na ɗauke ta ina fatan kuma na samu damar da zan zama babbar jarumar da zan cika burina. Kuma ko da ina son na yi suna a cikin harkar fim, ai sai na karɓu na yi sunan zan samu cikar burina. To ina fatan Allah ya bani damar da zan kasance ɗaya daga cikin fitattun jaruman da za su taka rawar gani a cikin harkar fim.
To ko kin fara ganin alamar cikar burin naki zuwa yanzu?
Maryam Salisu: Haka ne na fara ganin hakan, domin a yanzu ma akwai wasu ayyuka da na samu ba ɗaya ba biyu ba, waɗanda za a fara aikin a nan gaba kaɗan. Kuma abin da ya ba ni mamaki duk manyan finafinai ne waɗanda ina sa ran insha’Allahu za su fito da ni a matsayin ɗaya daga cikin jaruman da za a kalla a sabuwar shekarar nan ta 2026. Don ni kamar yadda na faɗa maka ina son na kai matakin da zan zama babbar jaruma ne, don ta haka ne zan samu cikar damar da nake so na taimaka wa na kusa da ni da ma waɗanda suke nesa suke buƙatar taimako. Idan son samu ne ma ina son na kasance ɗaya daga cikin fitattun mata da suke taimakawa al’umma ta ɓangarori daban-daban. Saboda ni dai da ka ganni ina da tausayin na ga wani yana cikin yanayi na buƙatar taimako, don haka na kan yi daidai karfina, to ina son na samu damar da zan rinƙa taimakawa masu buƙatar taimako, wannan shi ne cikar burina.
Harkar fim ana kallon sai mutum yana da ɗaurin gindi yake samun shiga ke da kika shigo harkar ya kika gani?
Maryam Salisu: Ni dai Alhamdulillah gata na Allah, kuma ɗaurin gindi na Allah, don haka ina da karfin gwiwar zan yi nasara a kan abin da na saka a gaba kuma bana shakka ko fargaba, da karfin ikon Allah zan yi nasara.
Yanzu idan za a ce ki bada shawara ga masu harkar fim, to wacce shawara za ki ba su?
Maryam Salisu: Ni kawai abin da nake gani da ɗan fim da wanda ba dan fim ba, duk inda mutum ya samu kansa, to ya yi ƙoƙarin kiyaye mutuncin sa, kuma mutane su gane ita fa rashin tarbiyya tun daga gida ake samun ta, babu yadda za a yi mutane su taso ba su da tarbiyya tun daga gidan su su zo suna rashin tarbiyya a fim kuma a ɗauka sai da suka shiga harkar fim suka samu rashin tarbiyya. To ni dai Alhamdulillah, na samu tarbiyya a gidan mu, don haka nake alfahari da kasancewar na tashi a gidan tarbiyya, saboda haka mutane su daina yin kuɗin goro suna cewa harkar fim babu tarbiyya a cikin ta. Kowace sana’a akwai masu tarbiyya akwai marasa tarbiyya, ya danganta ga yadda mutum ya tashi a gidan su, ina fatan mutane za su rinƙa yin adalci a cikin magungunan su.
To madalla mun gode.
Nima Nagode Sosai.
