September 18, 2026

Matsalar Fim Wani Lokaci Ba Daga Rubutun Labarin Take Ba. Cewar Bashir Ɗanrimi

0

A wannan lokacin babu wani marubucin labarin fim da yake tashe kamar Bashir Yusif Danrimi. Marubuci ne da ya fara tun daga rubutun Littafi tsawon lokaci a baya kafin ya rikide ya zama marubucin labarin fim.

Tun a wancan lokacin ya rubuta Littattafai da dama da suka shahara a wajen masu karatu wanda hakan ta ba shi damar zama marubucin labarin fim.

A yanzu da ya kasance a sahun gaba a cikin Marubutan da a ke yayin su a matsayin masu rubutun labarin fim, don kuwa yana da basirar rubutu a kan gajeren labari na fim da kuma fim mai dogon zango da labarin tarihin rayuwa

Sannan ya kasance guda daga cikin masu rubutun Shirin Dadin Kowa, Kwana Casa’in na Tashar Arewa 24 da sauran wasu finafinan da a ke haskawa a manyan gidajen talbijin.

Ganin yadda ya kasance kwararren marubucin labarin fim da kuma yadda a ke yin labarin fim a yanzu da ba su da tsari ya sa muka ji ta bakin sa domin jawo hankalin masu rubutun labarin a kan abin da ya kamata su in da ya fara da cewa

“Matsalar fim wani lokacin ba daga rubutun labarin fim take ba, saboda shi marubuci yana rubuta labarin sa ne daidai da fim din, amma wani lokaci a na samun matsala ne daga yadda aka yi kasafin kudin da za a yi fim din, to idan har kudin bai kai yadda labarin yake ba, to sai ka ga idan an zo aiki a na datsewa to kuma idan masu kallo sun ga matsala sai a dora ta a kan marubucin, don haka mutane su gane ba kowacce matsala ba ce ta marubucin labarin fim.

Duk da yake mu ma muna da tamu Matsalar ta rashin bincike da kuma yadda za a tsara labarin, domin babu yadda za a yi ka rubuta gida mai hawa uku ya ruguje a cikin fim irin namu don ka ga abu ne da ba zai shiga ba a cikin fim don haka mutum sai ya rubuta abin da ya san zai karɓu.

Kuma ina kira ga Marubutan mu na fim da su rinka neman ilimi da karatu domin ta haka ne za mu samar da labarin fim mai ma’ana da kuma ingancin da za mu rinka yin alfahari da shi a duniya.”

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *