Ranar Zaɓen Shugaban Ƙasa Nunfashin APC Zai Ƙarasa Ɗaukewa Cewar Mustapha Inuwa
Daraktan Yakin Neman Zaɓen Atiku Abubakar da Sanata Yakubu Lado a jihar Katsina Dakta Mustapha Inuwa ya faɗa da babbar murya cewa yanzu haka jami’yyar APC tana cikin mawuyacin hali tun bayan taron da suka yi na zuwa ɗan takarar shugaban ƙasa Atiku Abubakar a Katsina
Ya ce daga ranar da aka buga zaɓen shugaban ƙasa a ranar 25 ga watan Fabrairu jami’yyar APC zata yi ban kwana da wannan duniya, ya cewa yanzu haka tana cikin hali mutum kwakkwai rai kwaikwai (ICU)
Mustapha Inuwa ya yi wannan malamai ne a lokacin ƙaddamar da gangamin yakin neman zaɓen ‘yan takarar jam’iyyar PDP daga shugaban ƙasa zuwa ‘yan majalisa a garin Funtua ta jihar Katsina.
Ya kuma jan kunnen jama’a da su kauracewa zaɓen jami’yyar APC a zaɓe mai zuwa, yana mai cewa a ranar 25 Ga watan Fabrairu ne jami’yyar APC zata kwanta hagu, wato dai zata riga ‘yan uwanta jam’iyyu gidan gaskiya.
A cewar sa, idan jama’a na son ,zaman lafiya da kaunar a riƙa cin abinci gidansu sau uku, tare da yi wa ‘ya ‘yan su aure idan sun isa cikin kwanciyar hankali da lumana, kuma jama’a na san zuwa kasuwa da gona, da sauran hidimomi dole sai sun kori APC tun daga sama har ƙasa.
Daraktan ya yi jan hankali ga jama’a da su tabbatar sun yi wannan gagarumin aiki domin a cewar sa aiki ne da ya shafi kowa da kowa domin ganin an yi wa jami’yyar APC ƙamshin mutuwa ta yadda zata ida wucewa ba da shiri ba.
Haka kuma Dakta Mustapha Inuwa wanda tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina ne ya bayyana cewa taron da suka gudanar a garin Funtua taro ne na ra’ayi ba na tilas ba.
Haka kuma Daraktan ya ƙara da cewa taron da suka yi ya sha bambam da wanda jami’yyar APC ke yi, inda ya ce suna tursasawa Malaman makaranta da masu dafawa Yara abinci, da waɗanda ake ba tallafin Buhari suna zuwa taro ba da san ran su ba
Ya kara da cewa shi na so, taron na mutane ne masu ra’ayi kan su, musamman mutanen Funtua da aka sani tun fili azal da yin siyasar ra’ayi ba tursasawa ba.
