Zan Dawo Da Zaman Lafiya Kuka zaɓeni Gwamnan jihar Katsina 2023 – Sanata Yakubu Lado
Sanata Yakubu Lado ya bayyana cewa idan Allah ya sa ya kai ga samun nasarar lashe zaɓe, zai yi kokari matuƙa gaya wajan ganin ya kawar da rashin tsaro da ake fama da shi a jihar Katsina.
Ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar PDP ya bayyana haka ne a lokacin ƙaddamar da yaƙin gangamin zaɓen sa da sauran ‘yan takara a garin Funtua ta jihar Katsina
Ya ƙara da cewa yanzu dai kowa yana ji a jikinsa yana ganin irin abinda ke faruwa na matsin tattalin arziki wanda ya ce dole su tashi tsaye da addu’oi domin dawowar jami’yyar PDP akan mulki.
Kazalika Sanata Yakubu Lado ya ce jihar Katsina an santa a harkar noma amma yanzu komi ya lalace saboda haka ya yi alƙawarin dawowa da martabar noma a wannan yanki na Funtua.
Ɗan takarar gwamnan ya ce jami’yyar PDP tana da tausayi da kishin talaka wanda ya ce dole sai an haɗa hannu kowa da kowa sannan jami’yyar su ta PDP zata dawo bisa mulki.
“Idan Allah ya ba mu nasara duk alhairan da aka san jami’yyar PDP na yi a can baya, to zamu dawo da shi koma fiye da haka. Sannan ina yi wa jama’a albishir da cewa mutane za su dawo yin barci da idanu biyu” inji shi
Tunda farko da yake nashi jawabin, shugaban yakin neman zaɓen Atiku Abubakar da Sanata Yakubu Lado Sanata Umar Ibrahim Tsauri ya bayyana cewa idan aka zaɓi Lado da Atiku kamar an zaɓi zaman lafiya ne kwanciyar hankali da kuma ƙaruwar arziki.
Ya cigaba da cewa idan aka zaɓi Lado da Atiku kai tsaye an zaɓi ƙarshen matsalar tsaro da satar mutane domin neman kuɗin fansa ta yadda kowa iya barci harda da saleɓa.
“Idan kuka zaɓi jam’iyyar PDP kun zaɓi a biya wa ‘ya ‘yan ku kuɗin makaranta da baiwa manoma takin zamani kamar yadda aka saba a can baya sannan zai sakarwa ƙananan hukumomi mara su yi wa jama’a ayyukan alheri a faɗin jihar Katsina” inji shi
Sanata Umar Ibrahim Tsauri ya ƙara cewa idan jama’ar jihar Katsina suka zaɓi Atiku Abubakar da Lado tamkar sun zaɓi cigaban kiwon lafiya da maido al’umma yadda aka sameta ko ma fiye da yadda aka sameta a 2015.
