September 19, 2026

2023: Buhari Ya Umarci Ministocinshi Masu San Tsayawa Takara Suyi Murabus.

0

Muhammad Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin zaman majalissar zartaswa na yau Laraba.

Kamar yadda jaridar LEADERSHIP ta bayyana, zasu yi hakan ne kafin nan da zuwa ranar 16 ga watan Mayun wannan shekarar.

Ministocin Najeriya da abun ya shafa sun hada da ministan sufuri: Rotimi Amaechi, da ministan Niger Delta Godswill Akpabio da ministan kwadago da samar da guraben ayyukan yi Chris Ngige, da ministan kimiya da fasaha da kuma kere kere Ogbonnaya Onu, da ministan ilimi na kasa Emeka Nwajiuba, da ministan shara’a kuma babban atoni na gwamnatin tarayya Abubakar Malami.

Sauran sune ministan hako ma’adanai na kasa Uche Ogar, wanda ke neman kujerar gwamnan jihar Cross Rivers da kuma ministar kula da harkokin mata wadda ke neman kujerar sanata a jihar Plateau State.

Ministan yada labarai dai ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ma masu aike wa da rohotanni na fadar shugaban kasa jawabi bayan kammala zaman majalissar zartarwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *