Yajin Aiki: Majalisar Dattawa Za Ta Shiga Tsakanin Gwamnatin Tarayya Da Kungiyar ASUU.
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya sanata Ahmad Lawan ya ce majalisar za ta shiga tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta hanyar mayar da bangarorin biyu kan teburin tattaunawa a jiya Talata.
Lawan ya yi alkawarin ne ga jami’an kungiyar dalibai ta kasa (NANS), wanda Dr. Sunday Ndukwo Onuoha ya jagoranta zuwa ofishinsa.
Shugaban kungiyar daliban Sunday Asefon, wanda ya yi magana a madadin takwarorinsa, ya koka da yadda suke ci gaba da zama a gida tare da kawo cikas ga karatunsu, inda ya bukaci Shugaban Majalisar Dattawan da ya sa baki a cikin batun yajin aikin.
Da yake mayar da martani, shugaban majalisar ya nuna rashin jin dadinsa game da yadda lamarin ke tafiya, inda ya tunato cewa majalisar ta shiga tsakani a baya kafin abubuwa suyi kamar haka.
Jaridar LEADERSHIP ta ce, Sai dai ya yi alkawarin cewa majalisar dattawan za ta sake shiga cikin lamarin, tare da bayyana cewa nan ba da dadewa ba ne za a warware matsalolin.
Ya ce “Za mu yi kokari don ganin an dawo kan tebirin tattaunawa tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya domin a gaggauta warware matsalolin da a halin yanzu suka yi yawa suka hana mu bude Jami’o’inmu”.
“Amma ni ma ina son in yi kira gare ku, tunda za mu yi kokarin dawo da kowa kan teburin tattaunawa, ku ba mu dama mu yi hakan tare da ganin cewa za mu nemo mafita.
“Yanzu da kuka zo nan, za mu tabbatar da cewa duk wanda ke cikin wannan fanni musamman ma’aikatan gwamnati wadanda ke da alhaki sun fahimci juna.
Da yake mayar da martani kan barazanar da daliban ke yi na kawo cikas ga harkokin siyasa, Lawan ya yi kira gare su da su ci gaba da bin hanyar tuntubar juna tare da kaucewa yin taho-mu-gama.
“Abin da ya kamata mu yi shi ne mu ci gaba da bin hanyar tuntubar juna, hadin kai da kuma kaucewa gaba. Lokacin da kuke tuntuɓar, zai fi sauƙi a gare mu mu sami wani abu da za ku iya ƙarfafawa.
