September 19, 2026

Ina Nan Kan Bakana Na Yi Wa Katsina Katanga, Amma Ba Ta Bullo Da Siminti ba – Umar TATA

0

Daga El-Zaharadeen Umar

Ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a ƙarƙashin jam’iyar APC a zaɓen 2023 Umar Abdullahi Tata ya nanata kudirinsa na yi wa Katsina katanga domin magance matsalar tsaro da ta addabi wasu yankuna a jihar Katsina.

Idan za a yi tunawa Umar TATA ya yi wannan magana a kwanakin baya inda batun ya jawo cece ku ce musamman a kafar sadarwa ta zamani saboda ana ganin abin da wahala wai gurguwa da auran nesa.

To saida a jiya laraba Umar TATA ya ƙaddamar da takarar sa inda ya shirya baban taron sannan ya ziyarci ofishin jam’iyyar APC na jihar Katsina domin sanar da su kudirinsa na tsayawa takarar a kakar zaɓe mai zuwa.

A lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai an tambaye shi ko ina kudirinsa na batun yi wa jihar Katsina katanga da ya taɓa yi kuma batun ya tada kura musamman a kafafen sadarwa na zamani (Social Media)?

“Duk abinda zan yi in hana kashe mutum a jihar Katsina shi zan yi, na ce zan yi katanga ba wai katanga ce ta bullo ko rodi da siminti ba, a a duk yadda zan hana masu mashina shigowa cikin Katsina domin kashe jama’a ko kona dukiyarsu haka zan yi idan na zama gwamnan jihar Katsina” in ji Tata

” Idan ka ɗauka daga jibiya zuwa Faskari duka duka kilomita 250 ne sannan shi kan shi dajin da ‘yan ta’adda suke boyewa bai wuce kilomita 120 ba, to amma ba ina nufin zan yi katanga ta bullo ko rodi ba, zan yi amfani da duk wata dibara da fasaha in yaki matsslar tsaro a jihar Katsina..” inji Tata

Sannan ya yi ikirarin cewa zan yi amfani da ‘yan banga wajan tunkarar wannan ƙalubale ta hanyar tura mutum ɗari biyar a wasu ƙananan hukumomi da suke fama da matsanancin rashin tsaro a jihar Katsina.

Haka kuma ya ƙara da cewa ba zai yi sulhu da Kowane ɗan ta’adda ba, saboda a cewar sa ba a sulhu da wanda ya raina ka, babu yadda za a yi sulhu da mai kashe mutane kuma bai ajiye bindigarsa ba.

Ɗan takarar gwamnan ya cigaba da cewa ba zai taɓa bin tsarin yin sulhu da ɗan ta’adda ba, amma dai zai yi duk mai yiwuwa wajan ganin ya kare rayuka da dukiyoyin al’umma musamman ‘yan jihar Katsina.

Ya juya akan batun yadda zan bunƙasa tattalin arziki jihar Katsina kuwa Umar TATA ya bayyana cewa zai amfani da basirarsa wajan samar da fasahar hasken wutar lantarki mai karfin megawat 300 domin farfaɗo da masana’antu a jihar Katsina

Ya kuma ƙara da cewa zai samar da rukunin masana’antu (industrial layout) ya Shinfiɗa masu kwalta ta zamani sannan zai bayar da filaye kyauta ga kamfanoni domin ba su damar su gudanar da ayyukan da zai taimakawa wajan rage masu zaman kashe wando a jihar Katsina.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *