September 18, 2026

Ɗan Shekara 30 Ya Rataye Kansa A Jigawa.

0

Wani matashi dan shekara 30 da haihawa mai suna Usman Sanigoga da ke unguwar Akula a karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa ya rataye kansa.

Kakakin hukumar tsaron farin kaya ta Civil Defence a jihar Jigawa, Adamu Shehu ne ya bayyana hakan a Dutse ranar Alhamis 08 ga watan Junin 2023.

Ya bayyana cewa matar Sanigoga ta same shi a rataye a cikin dakin kwanansu ranar Laraba, yayin da ta dawo daga unguwa.

Ya kara da cewa matar ta bayyana cewa Sanigoga, mai sana’ar daukar hoto, ya ajiye ta a gidan wani dan uwanta a ranar Laraba da misalin karfe 2 na rana tare da yin alkawarin dawowa da yamma domin kai ta gida.

Bayan ta jira bai zo ba tai ta kiran wayarsa, amma bai amsa ba sai ta yanke shawarar komawa gida.

Ta kara da cewa ta iske gidan a kulle inda ta nemi taimakon mai abun hawan da ya kai ta ya hau katanga ya bude mata kofar shiga gudan.

“Da bude kofa, sai ta ga babur din mijinta yadda bata saba gani ba. Da sauri ta shiga ciki inda ta tarar da gawarsa a rataye a saman silin din dakin kwanansu.

“Ta fita daga gayyacinta dalilin abin da ta gani inda saidai direban mai abun hawan ya yi kururuwar neman agaji kafin makwabta su zo wurin,” kamar yadda ta shaida wa hukumar Civil Defence.

An garzaya da mjin zuwa asibiti inda likita ya tabbatar da rasuwar Sanigoga da isarsu.

Shehu ya bayyana cewa makusantan Sanigoga sun shaidawa hukumar NSCDC cewa yana fama da matsalar tabin hankali.

Ma’auratan sun yi aure kimanin watanni hudu da suka gabata kuma sun kasance tare da juna kafin faruwar lamarin, kamar yadda makwabta suka bayyana.

Hukumar Civil Defence ta fara gudanar da bincike kan lamarin, yayin da aka yi jana’izar mamacin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta Daily trust ta bayyana.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *