Dauda Dare Ya Jaddada Kudirin Gwamnatinsa Na ganin bayn ‘Yan Bindiga da suka addabi jihar
Daga Hussaini Ibrahim
Gwamman Jihar Zamfara,Dauda Lawal ya ya jadda kudirin gwamnatinsa na ganin bayan ‘yan bindiga da suka addabi al’ummar Jihar.
Dauda Lawal ya ba da wannan tabbacin ne a lokacin da ya ziyarci fadar mai martaba Sarkin Tsafe, Alhaji Muhammadu Bawa da ke karamar hukumar Tsafe,dan jajanta msu kan hare-haren da “yan bindiga da suka kai a Karamar hukumar Tsafe.
Babba mataimakin gwamnan aka kafafen yada labarai Suleman Bala Idrisa ne ya bayyyana haka a takardar da ya sa mahanu ga manema labarai a Gusau.
A cewar sa gwamna,Dauda Lawal ya jejanta wa al’ummar karamar hukumar Tsafe akan hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a baya-bayan nan.
Ya nuna damuwarsa kan yawaitar hare-hare a wasu yankunan jihar tare da tabbatar wa al’umma kudurinsa na ganin an magance matsalar”.
“Ina so in tabbatar wa mai martaba da jama’ar mu cewa tsaro shi ne babban abin da gwamnatina ta sa a gaba, shi ya sa muke hada kai da jami’an tsaro da abin ya shafa don ganin an samu zaman lafiya a jihar mu.
“Ni da sauran gwamnoni mun samu ganawa da Shugaban kasa, kuma na kawo masa maganar rashin tsaro a Zamfara. Shugaba Tinubu ya ba ni tabbacin goyon bayansa da jajircewarsa.na kuma bukaci sake ganawa da shugaban kasa a kokari na magance matsalar tsaro da ke addabar jihar mu.
“A lokacin da aka sanar da ni harin ‘yan bindigar a Tsafe, na tuntubi jami’an tsaron mu domin daukar mataki cikin gaggawa, kuma sunyi iyaka kokarin su alokacin.
Akan haka ne Gwamna Dauda yayi kira ga al’ummar Zamfara da su dage da addu’a babu dare ba rana dan samun nasarar ganin bayan ‘yan bindigan da suka addabi Jihar Zamfara.
Mai martaba Sarkin Tsafe, Alhaji Muhammadu Bawa, a nasa jawabin, ya gode wa gwamna Dauda Lawal, domin ya nuna matukar bakin cikin sa akan abunda ya same mu na hare hare.
“Ina so in nuna godiya da jinjina wa gwamna bisa wannan ziyarar da ba a shirya ba domin tausaya mana. ba zan iya boye farin cikina da na mutanen Tsafe ba, domin wannan shi ne karo na farko da wani gwamna ya kai ziyara domin jajanta mana hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa.
“Dole ne in jinjina wa jami’an tsaro da suka kawo saukin gaggawa dan kare al’ummar mu.
Kuma za mu bai wa sabuwar gwamnati dukkan goyon bayan da ya dace a yunkurinta na tabbatar da samun zaman lafiya afadin jihar Zamfara,” inji shi.
