Majalisa ta 10: Wase, Jaji Sun Kauracewa Ganawar Tinubu Da Yan majalisa Da Gwamnonin APC.
Yayin da taron kaddamar da majalisar wakilai ta 10 ke ƙara matsowa, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da zababbun Sanatoci na jam’iyyar APC, zababbun mambobin jam’iyyar APC, gwamnonin APC da shugabannin jam’iyyar kan batutuwan da suka shafi zaben shugabanni, kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta jaridar Daily trust ta bayyana.
An gudanar da taron ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja a daren Laraba bayan kammala taron majalisar wakilai ta 9.
Masu neman kujerar kakakin majalisar, Muktar Betara, Yusuf Adamu Gagdi, Miriam Onuoha da Sada Soli sun halarci taron.
Sai dai mataimakin shugaban majalisar, Ahmed Idris Wase da Aminu Sani Jaji wadanda suma ke neman kujerar ba su halarci zaman ba duk da an gayyace su zuwa taron.
An bada rohoton cewa shugaban kasar ya roki ‘yan majalisar da su marawa ‘yan takarar da jam’iyyar sa ta amince da su a matsayin shugabanci a majalisar dattawa da ta wakilai.
Ya yi magana kan bukatar ganin ‘yan majalisar dokokin APC sun yi kokari don ganin ‘yan takarar jam’iyyar APC da zasu shugabanci majalisa ta 10 sun samu nasara.
Don haka shugaban kasar ya bukace su da su yi aiki don ganin an bayyana Akpabio, Barau Abbas, da Kalu a matsayin shugabanni, yana mai cewa jam’iyyar ta zabo ‘yan takarar ne domin zaman lafiyar al’umma.
