November 19, 2026

Zuwaira Dauda Kolo za ta yi taron ƙaddamar da Littafin Taya ni mu gyara

FB_IMG_1760175400369

 

DAGA MUKHTAR YAKUBU

 

A yanzu haka dai shirye shirye sun fara yin nisa na taron ƙaddamar da Littafin Taya ni mu gyara, wanda shahararriyar marubuciya Zuwaira Dauda Kolo ta wallafa.

 

Taron ƙaddamarwar da za a yi shi idan Allah ya kaimu ranar 8 ga Nuwamba 2025 a Ɗakin Taro na Gidan Mambayya da ke Unguwar Gwammaja a cikin Birnin Kano..

 

Ana sa ran manyan baki daga ciki da wajen Ƙasar nan za su halarci wajen taron.

 

Zuwaira Dauda Kolo dai wadda aka fi sani da likitar Ma’aurata tsohuwar marubuciya ce da ta dade tana yin rubuce-rubuce na littattafai wanda ta rubuta littattafai kamar Mardiyya, Bulalar zuciya, Zubar Hawayena, Kada Daya, Na gane duniya. Da sauran su.

 

Bayaga rubutun Littattafai ta shahara a Soshiyal Midiya, a wajen rubuce rubuce, a kan al’umuran mata da kuma kiwon lafiya.

About The Author