Ghali El-Abdallah DZ Ya zama Shugaban gidan Talbijinna Hijrah
DAGA MUKHTAR YAKUBU
Hukumar gudanarwar ta tashar gidan talabijin ta Hijrah Tv ta tabbatar da nadin Ghali El-Abdallah DZ a matsayin sabon Manajan Darakta na tashar wato (MD)
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da hukumar gidan Talbijin din suka rabawa manema labarai , Shugaban gidan Talbijin na Hijrah a cikin sanarwar yace “sun yi wannan nadin duba da irin gwagwarmayar da Ghali El-Abdallah DZ ya yi a gidajen rediyo da dama da kuma gwagwarmayar da ya yi a masana’antar Kannywood.
Wannan dalilai ya sa suka tabbatar da yana muhimmiyar gudummawar da zai baiwa tashar Hijrah TV a irin wannan lokaci.
Ghali El-Abdallah dai fitaccen Mawaki ne furodusa kuma jarumi a Kannywood, wanda aka haifa a Unguwar Durumin Zungura dake cikin birnin Kano , a shekarar 1978 inda ya yi Makarantar Firamare din sa a Kwalli Kuma ya yi Karamar Sakandare a Sabuwar Kofa sai Babbar Sakandare a Kwalejin Rumfa duk a cikin birnin Kano.
Ya ci gaba a Kwalejin Sa’adatu Rimi inda ya yi NCE. Sai kuma ya tafi Jami’ar Bayero inda ya yi Babbar Difloma a fannin aikin Jarida.
A bangaren aiki kuwa ya yi aiki a Gidan rediyon Freedom F M da gidan rediyon Rahama F Mda gidan rediyon Arewa Sai Kannywood Series T V , d a kuma Hijira TV Wanda a yanzu yake a matsayin Manajan Darakta.
A Masana’antar Kannywood Kuma Ghali El-Abdallah D Z ya kasance komai da ruwan ka. Inda ya fara da wakokin tallace tallace, da na wayar da kai. Sai kuma shirin sa mai farin jini na Dandalin fasaha wanda yake hira da Mawaka da ‘yan fim.
Sannan shi ne marubuci kuma jagoran shirya wasan kwaikwayo na Birnin Dala a Dala F M, sai kuma wasan kwaikwayo na Ƙasar Jallaba a tashar Arewa FM wadda daga baya aka yi fim din wasan kwaikwayon da sunan Mai martaba , Fim din da ya shiga jerin finafinan da suka wakilci Nijeriya a gasar Oscar a Ƙasar Amerika.
