Zaɓen 2023: Angulu Da Kan Zabo Zan Yi A Dutsinma. Cewar Umar TATA
Ɗaya daga cikin ‘yan takarar gwamnan jihar Katsina ƙarƙashin jam’iyyar APC Umar Abdullahi Tata ya bayyana a shafin sa na Facebook cewa ba zai fifita jami’yya
ba fiye da ɗan gida.
Umar Tata dai na zama na biyun karshe a zaɓan fidda gwani inda ya tashi da kuri’a takwas a ya yin da wanda ya zo na ɗaya yana da kuri’a dari hudu da ɗoriya.
Sai dai a rubutun na shi, ya bayyana cewa shi jigo ne a jam’iyyar APC amma haka ba zai hana shi ya goyi bayan ɗan takarar majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Dutsinma da Kurfi ba duk da cewa ba jami’yyar su ɗaya, amma dai garin su ɗaya.
‘Daga cikin mutane 6 da suka taɓa riƙe wannan kujerar a tsawon shekarun nan 24 ba a taɓa ɗan majalisa wanda ya riƙe wannan kujerar kuma yayi ma constituency ɗin shi aiki na Dutsinma /Kurfi ba irin AY. Projects kadai within wannan shekarun 3 da ɗoriya da yayi yayi 86 for a first timer.”
Ya cigaba da cewa kuna zaton me zai faru in ya samu seniority na komawa tunda ita kujerar majalisa tafi karfi da amfanuwar jama’a ga wanda ya koma, ya ƙara kuma ya kara.
A cewar Umar Tata duk isar Ahmed Babba Kaita da Muntari Ɗan Dutse saboda fa haka ne to mu me zai hana muyi haka sai ace kullum sau ɗaya ake hawan wannan kujerar kamar mutanen da basu san ciwon kan su ba! When will we ever grow like this? Ai babu sakamako ga alkhairi face alkhairi.
Haka dai Umar Tata ya cigaba da amayar da irin abubuwan da ke cikin ransa game da wannan mataki da ake ganin bashi da maraba da angulu da kan zabo a siyasa, wato kana yin jami’yyar a wancan mataki amma baka yi a wancan mataki.
Tata ya ƙara da cewa a dai wannan karon a kuma kan kujerar federal House of Reps I am choosing Dutsinma above party and I am going with Armaya’u na jam’iyyar NNPP in Dutsinma zata faɗi to na shirya mu durmuye tare amma ba zanci amanar ta ba haka ba zan wulakanta ta da ɗan da ta haifa ba.
Aminu Dan Arewa ɗan takarar majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Dutsinma da Kurfi a ƙarƙashin jam’iyar APC abokina ne kuma bani da matsala kowace iri da shi amman a Musulunci kishi farilla ne.
a karshe dai Umar Abdullahi Tata ya ce wanda ya yi ma ba daidai ba sai dai ya yi hakuri don Allah.
