September 18, 2026

Wata Sabuwa: DSS Ne Suka Hana Shema Zuwan Taron Atiku Abubakar A Katsina. Cewar PDP Tsagin Gwamna Shema

0

Jam’iyyar PDP tsagin tsohon gwamnan jihar Katsina Barista Ibrahim Shehu Shema sun bayyana dalilin da yasa ba a Shema ba a ranar da Atiku Abubakar ya zo Katsina domin yaƙin neman zaɓen sa a watan Disamba 2023.

A ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na jam’iyyar PDP na ƙaramar hukumar Katsina Zaharadeen Ɗan Mulki ya ce shugaban hukumar DSS na jihar Katsina ne ya kira gwamna Shema Ya bashi shawarar kadda ya halarci taron don gujewa samun matsala.

Ɗan Mulki dai na yin wadannan kalamai a matsayin martani bisa wasu Zarge-Zarge da Alhaji Lawal ɗan Ade ya yi wa tsohon gwamnan wanda ya ce ba masoyin Atiku ba ne na gaskiya tunda ba a ganshi ba ranar da Atiku ya zo Katsina.

Bisa haka ne Zaharadeen Ɗan Mulki ya bada wancan amsa, haka kuma ɗan Mulki ya musanta cewa akwai matsala tsakanin gwamna Shema da kuma ɗan takarar gwamnan a ƙarƙashin jam’iyar PDP Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke da ake ganin kamar sun kai ruwa rana da tsagin tsohon gwamnan.

Kakakin na jam’iyyar PDP ya ce dukkanin Zarge-Zarge da Lawal Ɗan Ade ya yi wa Shema ba su da tushe balanta makama hasali ma Lawal Ɗan Ade ya bar PDP ya koma jam’iyyar mai kara gwari.

Tunda farko a hirar sa da manema labarai Lawal Ɗan Ade ya yi amfani da wata murya da aka made wanda ya ce wasu makusantan gwamna Shema ne suka bayyana irin ta’asar da ake tafka a lokacin mulkin sa, inda har ya ce kimanin naira tiraliyan ta yi sama ko ƙasa.

Sai dai a martanin na shi, Zaharadeen Ɗan Mulki ya ce mutumin da ba ɗan jami’yyar PDP bane bai ga dalilin bashi amsa ba, amma dai wanda magana ce kawai ta ‘yan siyasa inda kowa ke ganin ya isa ya yi magana da bata da asali ko alama.

Ɗan Mulki ya ce sauraran Lawal Ɗan Ade baya da banbanci da wakokin Ado Gwanja, sannan ya ja kunnen sa da ya tafi Jami’yyar su ta kayan gwari tunda ya bar jami’yyar PDP.

Duk acikin hirar ta sa, Lawal Ɗan Ade ya bayyana Shema a matsayin mutum marar takawali inda yayi kira gareshi tare da yaransa da zo ayi tafiyar da da su ba wai su koma gefe suna surutai ba.

Lawal Ɗan Ade ya kuma zargi tsohon shugaban jam’iyyar PDP Hon. Salisu Yusuf Majigiri da yin uwa makarɓiya wajan tafiyar da PDP wanda ya so kashe ta, ta hanyar korar duk wani mai faɗa aji acikin jami’yyar PDP.

Shima a nashi martanin Zaharadeen Ɗan Mulki ya ce ɗan Ade bai san abinda ke tafiyar a wannan jami’yyar harma ya yi zargin wasu suke turo shi domin ya ci mutuncin manyan mutane irinsu tsohon gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shehu Shema da sauransu.

Yanzu haka jama’a sun fara yarda da cewa lallai akwai abinda ke faruwa domin ba a ganin tsagin tsohon gwamnan a tafiyar ɗan takarar gwamnan Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *