September 17, 2026

Zanga Zangar Ƙungiyar NLC a Zamfara, Majalisar Dokoki Ta Shiga Tsakani

0

Daga Hussaini Yero, Gusau

Masu iya magana na cewa, rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, yau saura mako guda ke nan wa’adin da majalisar dokokin jihar Zamfara ta ɗauka, ƙarƙashin shugaban majalisar Hon Mu’azu Magarya na sasanta kungiyar Kwadago watau (NLC) reshen jihar Zamfara, Ƙarƙashin jagoranci , Kwamaret Sani Haliru da gwamnatin Jihar Zamfara, Karkashin Jagoranci gwamna Bello Matawale Maradun.

Majalisar dokokin jihar Zamfara,ta shiga sulhu ne tsakaninta da kungiyar kwadago , sakamakon shirya gagarimin zanga -zanga dan bayyana wa duniya halin da ma’ainatan jihar ke cikin na mawuyacin hali da kin basu hakokin su da gwamnatin duk da matakan sulhu da tattaunawa da jami’an gwamnatin da kungiyar Kwadago ta sha yi wanda babu adadi amma gwamnatin ta yi watsi da su kai kace ba sune zuciyar gwamnatin jihar ba .

Zaman sulhun da kungiyar kwadago da yarjejeniyar dage zanza zangar na ɗauke ne a takardar da ma’taimakin Kilak , Muhammad Aliyu ya sanya ma hannun a ranar 30/03/2022, wace majalisar dokokin ta aikawa shugaban kungiyar kwadago kwamaret Sani Haliru.

Abinciken da wakilinmu ya yi kan batun zanga-zangar, lallai shugabannin ma’ainatan jihar Zamfara, na kowane ɓangare sun shirya tsaf akan batun zanga zangar ko a mutu ko ayi rai sakamakon watsi da hakokin ma’aikatan da doka tace abasu ba alfarma ba musamman ma ma’aikatan ƙananan hukumomi da har yanzu akwai masu amsar karancin albashi na dubu shida, bama na dubu sha takwas ba ko talatin ba

Haka suma tsafin ma’ainatan ‘yan fensho suma suna cikin tsaka mai wuya wajan biyan kuɗin fensho na wata-wata ana samun tsaiko bama batun kuɗin sallamar su na aiki ba .

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *