September 16, 2026

Isra’ila ta zargi Falasɗinawa da lalata Ƙabarin Annabi Yusuf

0

Daga: Comrade Musa Garba Augie

Mahukuntan Isra’ila sun ce Falasdinawa sun lalata wani wuri mai tsarki na Yahudawa a Nablus, a yayin da rikici ke ƙara ƙamari tsakanin Falasdinawa da sojojin Isra’ila a yankin gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye.

Wani shafin Twitter na gwamnatin Isra’ila ya wallafa wani bidiyo da ya ce ke nuna yadda Falasdinawa ke kai hari a wurin da Yahudawa ke ganin ya ƙunshi ƙabari Annabi Yusuf.

Zuwa yanzu babu wani martani daga wata ɓangarorin Falasdinawa.

Yahudawa na girmama wurin da ƙabarin yake, amma yana cikin yankin Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye.

An sha yin arangama a wurin, har ta kai aka ƙona kafin aka sake gyarawa.

Ministan tsaron Isra’ila Benny Gantz ya bayyana al’amarin a matsayin “babban laifin saɓa ƴancin ibadah.”

Yankin Yamma da Kogin Jordan na fuskantar barazanar tsaro tun bayan farmakin da sojojin Isra’ila suka ƙaddamar bayan harin da aka kai a Tel Aviv da kuma cikin yankin Isra’ila.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *