September 17, 2026

An Yi Kira Ga Matasa A Jihar Katsina Su Fiddo Hazaƙarsu Ta Hanyar Amfani Da Fasahar Zamani.

0

An yi kira ga matasa a jihar Katsina su rungumi fasahar zamani wajen fitowa da hazaƙarsu, tare da shiga cikin ƙanana da matsakaitan sana’o’i.

 

Mataimakin gwamnan jihar Katsina Faruq Lawal Jobe ya bayyana hakan a lokacin buɗe taron bunƙasa sana’o’i na kwanaki 3 da hukumar bunƙasa sana’o’i ta jihar Katsina ta shirya.

 

Mataimakin gwamnan ya taya waɗanda suka halarci taron murna bisa ɗaukar matakin rungumar ƙirƙire-ƙirƙiren zamani a ƙanana da manyan sana’o’i wanda shi ne ƙashin bayan tattalin arziki daga tushe.

 

Faruq Lawal ya ƙarfafa gwiwar waɗanda suka halarci taron da cewa su tunkare shi da karsashi, tare da maida hankali su koya, haɗi da yin amfani da ilimin da suka samu ya yadda ya kamata a harkokinsu na kasuwa.

 

Ya yaba ma waɗanda suka shirya taron bada horon bisa nuna hangen nesa wajen sanya matasa a hanyoyin zamani masu riba na yin kasuwanci domin zama masu dogaro da kai.

 

A tsokacinta shugabar hukumar bunƙasa sana’o’i ta jihar Katsina A’isha Aminu Malumfashi ta ce ƙirƙire-ƙirƙiren zamani sun ƙunshi fasaha da yin abubuwa a aikace da zasu bada damar ƙirƙirar sabon abu.

 

A’isha Aminu Malumfashi ta bayyana cewa taron mai taken “fitowa da hazaƙa” na jawo hankalin gwamnati mai ci yanzu wajen fitowa da hazaƙar da ke cikin ƙanana da matsakaitan sana’o’i ta hanyar amsar tsarin ƙirƙire-ƙirƙiren zamani.

 

Wakilin shugaban hukumar bunƙasa bayana na fasaha ta ƙasa Salisu Kallah ya yi nuni da cewa taken taron ya yi daidai da ƙudurin sauyi na gwamnati mai ci yanzu wanda ya maida hankali kan mahimmancin ƙanana da matsakaitan sana’o’i.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *