Kwamitin Farfaɗo Da Kamfanin Ƙonannen Bulo Na Funtua Ya Fara Aikinsa.
Kwamitin Farfaɗo da ayyukan Kamfanin yin ƙonannen bulo na Funtua ya fara gudanar da aikin sa.
Shugaban Kwamitin farfaɗo da Kamfanin yin ƙonsnnen bulon na Funtua-wato Funtua Bricks Works Limited Alhaji Garba Faskari ya yi taro da masu ruwa da tsaki kuma Mambobin kwamitin kan yadda za a farfaɗo da kamfanin don cigaba da aiki yadda ya kamata, don amfanin al’umma.
Alhaji Abdullahi Garba Faskari wanda kuma shi ne sakataren gwamnatin jihar Katsina ya bayyana cewa, taron ya maida hankali ne kan gano matakin da kamfanin ya ke ciki da kuma gano yadda aikace-aikacensa ke gudana.
Ya bayyana cewa haka zalika taron ya maida hankali ne kan gano hanyoyin da zai shawarci gwamnati akan hanyoyin da za a bi domin samun nasarar farfado da shi.
A cewar sa, kwamitin ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen shigo da duk wani mutum da zai bada gudunmawa domin ganin aikin da aka sanya kwamitin ya cimma nasara.
An dai baiwa kwamitin wa’adin makonni 4 da ya kammala bincikensa gami da miƙa rahoto kan aikin da aka bashi.
