September 18, 2026

Zan Maidama Tsaro Da Tattalin Arzuki Hankali — Osinbajo.

0

Mataimakin shuganan Najeriya Yemi Osinbajo ya yi alkawalin ci gaba daga inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsaya idan aka zabe shi shugaban kasa a babban zaben shekarar 2023 dake tafe.

Mataimakin shugaban kasar ya yi wannan alkawalin ne a lokacin da ya kai ziyara ga sarkin Katsina Alhaji Abdulmummuni Kabir Usman a fadarshi.

Ya fada ma sarkin cewa, aiki da suka yi tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari yasa ya samu hikimar sanin yadda zai mulki kasar nan.

Kamar yadda ya bayyana, rikon kwarya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke bashi idan ya yi tafiya ya koya mashi darussan sanin shugabanci, dama sanin halin da Najeriya ta ke ciki.

Professor Yemi Osinbajo ya yi alkawalin cewa, zai saka batun tsaro da sha’anin tattalin arzuki gaba idan aka zabe shi.

Ya kuma koka kan yadda matsalar tsaro ke zama karfen kafa ga tattalin arzuki masamman ma noma, tare da bayyana cewa, za a daukar ma lamarin matakan da suka kamata don ganin an magance matsalar.

Mai san a zabe shi shugaban kasar ya ce ziyarar shi zuwa jihar Katsina nada nufin tattaunawa da wakilan masu zabe wato delegates, wanda su ne za su zabi a matsayin dan takarar shugaban kasa a karkashin tutar jam’iyar APC.

Tunda farko, saida gwamna Aminu Bello Masari wanda ya jagoranci mataimakain shugaban kasar zuwa fadar sarkin Katsinan, ya ce Osinbajo ya zo jihar Katsina ne domin neman goyan bayan wakilan masu zabe gabanin babban zaben shekarar 2023 dake tafe.

Gwamna Aminu Bello Masari ya ce mataimakin shugaban kasar yanzu ya jona sahun masu neman shugabancin kasar nan.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *