Kungiyar 13X13 Na Hasashen Mutum Miliyan 10 Za su Amfana Da Ita -Rarara
Shugaban kungiyar 13X13 na ƙasa Dauda Abdullahi Kahutu Rarara ya bayyana cewa ana sa ran mutane fiye da miliyan goma za su iya cin abinci a ƙarƙashin wannan tafiya ta 13 X 13.
Rarara ya faɗi haka a lokacin wani gagarumin bikin rarraba kayayyakin abinci da wata kungiya mai suna “Buhari For All” ta baiwa kungiyar 13X13 tun cikin azumi amma wasu dalilai suka hana raba kayayyakin sai wannan lokaci.
Kayayyakin kamar yadda Dauda Kahutu ya faɗa sun haɗa da shinkafa rabin mota da kuma masara mota guda wanda aka rabawa dukkanin ‘ya ‘yan kungiyar tare da kuɗi naira duba ashirin kowane.
Ya ƙara da cewa kowane mamba da wannan kungiyar sai samu buhun shinkafa uku mai nauyin kilo 10 sai buhun masara huɗu mai nauyin kilo 25 da kuma kuɗi naira duba ashirin.
“Koda a tsakaninmu zamu san yadda za mu yi domin riƙe wannan kungiyar da kuma tafiyar 13X13 tare da ita kanta masana’antar finafinai baki ɗaya” inji shi
Ya ce ya zuwa yanzu wannan kungiya ta 13X13 ta ɗauki matsaya da layi domin tsayuwa da ƙafafuwanta ta hanyoyin da damu acikin wannan masana’anta ta industiri.
“A wannan tafiya ta 13X13 zamu riƙe shirya wassani a lokuta daban daban sannan zamu riƙe karɓar kwangila mu yi a biya mu, haka kuma muna iya yin kwadago a biya mu domin mu samu kuɗaɗen shiga a wannan tafiya ta mu” inji Rarara
Shugaban kungiyar 13X13 na ƙasa ya bayyana cewa sune ya kamata ace suna taimakawa jama’a ba wai su tsaya jiran na jama’a ba, kasancewar suna da kowane irin mutum a cikin masana’antar su ta fuskar basira da hikima da kuma ilhama.
Ya ce daga cikin abubuwan da za su cigaba da yin acikin tafiyar 13X13 sun haɗa da zuwa gidan gyaran Hali da gidan Marayu da mayar da yara makaranta da ba su tallafi da taimakon su kan su ‘ya ‘ yan wannan masana’anta ta industiri baki ɗaya.
