September 18, 2026

Zamu Yi Amfani Da Albarkatun Mu Yadda Ya Kamata — Shugaban Ƙaramar Hukumar Mani.

0

Daga Auwal Isah

Karamar Hukumar Mani ta bayyana shirinta nayin amfani da albarkatun da karamar hukumar ta ke da su bisa gaskiya da adalci domin samar da cigaba mai ma’ana a yan’kin.

Shugaban karamar hukumar Dr. Yunusa Saleh Bagiwa ya bada tabbacin hakan a lokacin wani taro da mataimakin shugaban karamar hukumar da kuma kansiloli 11 da ya gudana a ofishin sa.

Dr. Yunusa Sale Bagiwa ya jaddada cewa, bunkasa ayyukan more rayuwa, da inganta kiwon lafiya, da bunkasa ilimi, da samar da ruwa, da magance rashin aikin yi za su kasance ginshikan da zai maida ma hankali.

Ya jaddada cewa, za a bullo da shirye shiryen tallafa wa matasa da mata domin su zamo jakadu na gari kuma masu dogaro da kai a cikin alumma.

Shugaban karamar hukumar ya kara da cewa kokarin mulkin karamar hukumar na yanzu shi ne tallafa wa kokarin gwamnati mai ci yanzu domin bunkasa tattalin arziki tun daga tushe.

Ya kuma yaba ma gwamna Masari bisa gudanar da ayyukan cigaba da suka hada da shinfida hanyoyi, da samar da ruwa kiwon lafiya, da ilimi, da tallafa wa matasa da mata.

Dr. Yunusa Saleh ya kuma yaba ma gwamnatin jiha akan shirin nan da ta ke yi a halin yanzu, wanda ya baiwa yan asalin karamar hukumar Mani dubu 12 damar karba naira 40,000 kowannensu domin bunkasa sana’o’i.

Shima da ya ke jawabi shugaban kansilolin karamar hukumar Alhaji Yusuf Haruna Bagiwa ya bukaci sauran jami’an karamar hukumar da su rubanya kokarin da suke wajen ciyar da karamar hukumar gaba.

Alhaji Yusuf Haruna ya yi nuni da cewa, tare da kyawawan akidu na sabon shugaban karamar hukumar, hadin gwaiwa da masu ruwa da tsaki, da al’ummar yankin za su samu cigaba mai ma’ana.

Daga nan sai ya jaddada bukatar da ke akwai ga alumma na s bayar da gudumuwa domin cimma manufar da ake son cimmawa.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *