Za A Dawo Kai Gaisuwar Sallah Ga Shugaban Ƙasa.
Fadar shugaban Najeriya ta ce za a dawo da kai gaisuwar sallah da aka saba yi ma shugaban kasa a Abuja a baya, wadda kuma aka hana shekaru 2 da suka gabata sakamakon bullar cutar Corona.
Saidai fadar shugaban kasar ta ce wadanda aka gayyata domin su kai gaisuwa, za su sanya takunkumin rufe baki da hanci, tare da yo awo da kuma dawowa da shaidar da ke nuna cewa mutum ba ya dauke da cutar Corona a cibiyar yin taro ta fadar shugaban kasar a matsayin sharuddan da za a ciki domin shiga wurin kai gaisuwar.
A cikin wata sanarwa da aka fitar, an bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai amshi bakuncin masu kawo gaisuwar kimanin 100 a dakin taro ma fadar shugaban kasar da misalin karfe 03:00 na rana a ranar Sallah.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, ministan birnin tarayya Abuja Muhammad Musa Bello, da sakataren gwamnatin tarayya, da sanatoci, da shugaban ma’aikata, da dai sauransu, su ne za su jagoranci wadanda aka gayyatan zuwa kai gaisuwar.
Sauran sun hada da shugabannin bangaren shari’a na Abuja, da membobin majalissar zartarwa, da manyan hafsosin tsaron da sauran shugabannin jami’an tsaro na kasa, da Musulmai da Christoci da ke Abujar, da shugabanni majalissun Abuja, da kuma masu rike da sarautun gargajiya.
