Zamu Haɗa Kai Da Ƙwararu Domin Kawo Ci gaba a Kannywood. Cewar Sunusi Oscar 442
Sabon Babban mataimaki ga gwamnan jihar Kano kan masana”antar Kannywood Sunusi Hafiz Oscar 442, ya sha alwashin kawo ci gaba da kuma bunƙasa harkar ta fim a ƙarƙashin ofishin sa na Babban mataimakin na musamman da gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba shi.
Sunusi Oscar ya yi wannan kalamin ne a tattauwar su da wakilin mu lokacin da ya ke tambayar sa a kan kowanne irin ci gaba harkar fim za ta samu ta ƙarƙashin ofishin sa?
“Wato shi wannan muƙami da mai girma gwamna ya bani muƙami ne, da zai yi aiki akna ita masana’antar, wato shi gwamna ya na buƙatar Mutum da zai rinƙa ba shi shawara da gudammawa na labaran cikin ta musamman abin da ya shafi ci gaba da kuma abubuwan da aka samu naƙasu a cikin su, domin a tallafa mata zuwa gaba daga nakasun da ta samu a shekaru takwas da ta yi a hannun tsohuwar gwamnati, to wannan shi ne dalilin da ya sa ya yi wannan muƙami.
Kuma ita wannan masana’antar, a yanzu za ta amfani abubuwa sosai da wannan muƙami, don duk wata hanyar da a ke bi a samar da ci gaba to wannan masana’antar za mu kai ta ga wajen domin mu na cikin wannan masana’antar shekara da shekaru.
Oscar ya cigaba da cewa don haka mun san abin da ya ke damun ta kuma muna cikin wannan tsari, don haka za mu yi ƙoƙari in Allah ya yarda mu sanar wa da gwamnati abin da ya ke damun ta. Kuma in sha Allahu wannan gwamnati za ta share mana hawayen mu.”
Da muka tambaye shi ko me ya bambanta ofishin sa da na Hukumar tace finafinai kuwa cewa ya yi.
“Ai abubuwan da suka bambanta mu su na da yawa, shi aikin Hukumar tace finafinai shi ne a kai fim su duba su tace shi su tabbatar da ingancin sa tare da bada izinin fitar da shi don kada abin da za a fitar ya zama ya saba da addini ko al’adarmu da sauran wasu abubuwa da doka ta ba su damar aiwatarwa.
Amma shi ofishina duk wani abu da ya shafi masana’antar ya na ƙarƙashin ofishin mu, saman ta da tsakiyar ta da kumu ƙasa duk abin da shafi harkar ita masana”antar, to mu muna da ruwa da tsaki da shi.”
Ko wanne irin shiri Oscar ya yi na kawo gyara a cikin harkar fim?
“To mu daman a shirye mu ke,, domin abu ne da ya daɗe ya na damun mu tun ba yau ba, kuma a yanzu da Allah ya ba mu wannan dama, in sha Allah za mu yi amfani da ita mu ga mun taimaki ita wannan masana’antar ta inda duk ya kamata. Kuma za mu yi tuntuɓa daga wajen jagororin mu ɗaya bayan ɗaya, kowanne za mu ji abubuwan da ya kamata su taimaka sqboda a taimaki masana’antar. Haka kuma Za mu ɗauki abu na gaskiya mu ajiye wanda ba na gaskiya ba mu yi amfani da abin da ya dace, mu kai wa gwamnati shi domin ci gaban masana’antar”.
Da yake kai dan fim ne ko wanne sauyi ka ke ganin za ka samar fiye da wanda a ke gani a yanzu cikin harkar fim?
“Za mu yi kallo duba da yadda zamani ya canza, kuma za mu yi bakin kokarin mu don ganin mun tafiyar da wannan masana’anta a zamanance kamar yadda duniya ta canza, mu ma muna fatan wannan masana’anta ta canza domin har yanzu mu na nan a karamin matakin da Tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ya tafi ya bar mu.
Mun yi zaton wannan Gwamnatin ta Gwanduje da ta zo za ta dora sai ya zamanto sana’ar ma ta gagara babu ita ya zama an tarwatsa ‘yan kasuwa, aka saka musu tsoro da kama na kamawa. To ka ga tun da mai saya ba ya nan, idan ka dakko kaya ina za ka kai?
To saboda haka su ma wadanda su ke tsarawar su ma sai aka fara bin su.
Masu bada Umarni irin mu. Mu ma aka bi a na kama mu daya bayan daya aka sa matsorata, wani ko ba ya son tsarin, haka ya hakura ya bi domin ya na ganin idan bai bi tsarin ba za a kama shi, tun ba ya so haka ya hakura ya bi. Amma mu da muka gane cewar wannan tsarin da aka fara ya na da karshe, to duk irin wahalar da muka sha babu ja baya haka muka hakura har Allah ya kawo mu ga wannan lokacin yanzu ga shi Allah ya sa maigirma Gwamna ya ba ni mukami a wannan masana’antar, kuma za mu hada kai da duk wanda ya ke son ci gaba a cikin wannan masana’anta, mu hada kai mu kawo ci gaba baki daya.”
Da yake zamani ya canza an samu ci gaba ta fuskar kasuwar da ma yadda a ke shirya fim din wanne irin gyara za ku samar a cikin harkar?
“To shi ne abin da na fada maka a baya cewar za mu yi tuntuba ta duk inda ya kamata a wajen masana domin mu kai wannan masana’antar gaba. Ba mu za mu yi ba, mu namu wato gabatarwa ne,don haka za mu nemi masana su ba mu shawara da kuma abin da muka sani, mu tattara shi, mu kai wa maigirma Gwamna, kuma mun san daga mun kai in sha Allahu Gwamnati za ta share mana hawayen mu.
Don haka ina godiya ga Allah da ya sanyya nake da wannan muƙami a yanzu na babban maitaimaki ga gwamna kan masana’antar kannywood kuma Ina godiya ga maigirma gwamna Abba Kabir Yusuf tare da Madugun Ɗariƙar Kwankwasiyya Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso bisa wannan muƙami da suka ba ni. Allah ya saka musu da alheri, Allah ya sa rayuwar su ta gaba ta yi kyau, ya kawo musu babban rabon da ya fi wanda su ke Kai a yanzu.”.
