September 17, 2026

Gwamnatin Zamfara Zata Magance Matsalar Ilimi A Fadin Jihar

0

Daga Hussaini Ibrahim

Gwamnatin Jihar Zamfara, karkashin jagorancin gwamna Dauda Lawal ta dukufa wajen ganin an kawo karshen matsalar ilimi a jihar.

Sabon kwamishinan ilimi da kimiya da fasaha da aka rantsar, Mallam Wadatau Madawaki, ya bayyyana haka a lokacin da ya ke amsa tanbayoyin manema labarai a Gusau.

Kwamishainan ya bayyyana cewa, ilimi a jihar na bukatar kulawa cikin gaggawa domin ganin an yi wa tsarin garambawul, ta yadda Zamfara za ta yi gogayya da takwarorinta wajen bunkasar Ilimi.

Kwamishinan ya yi la’akari da cewa ingantaccen ilimi, musamman kan kimiyya da fasaha shine farko don ci gaban zamani musamman wajen ƙarfafa matasa a fannin ilimin fasaha wanda zai kawo tsarin sauyi na tattalin arziki.

Kuma Ilimin Fasaha ne kangaba a wannan zamani namu wanda shi kadai Idan mutum ya sameshi zai iya dogara da shi ba tare da aikin gwamnati ba.

Kwamishina Wadatau ya kuma tabbatar da cewa, matakin farki shine gyara Ilimin firamare dan sai da kyakyawan fandeshin ne gini ke inganta idan babu tsari mai kyau Firamare da Sakandire yaran Babu inda zasu iya zuwa a fagen karatu.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *