Jam’iyyar NNPP Ta Dakatar Da Kwankwaso Bisa Zargin Yin Zagon Ƙasa
Kwamitin amintattun jam’iyyar NNPP na kasa ya dakatar da jagoran kuma dan takarar shugaban kasa jam’iyyar a zaben da ya gabata, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, bisa zargin yi wa jam’iyyar zagon kasa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya watau (NAN), ya ruwaito cewar dakatarwar za ta yi aiki ne har na tsawon watanni shidda masu zuwa daga yau Talata.
Haka zalika, Kwamitin amintattun jam’iyyar ya sanar da naɗa Dakta Agbo Major a matsayin mai riƙon kwaryar muƙamin shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, sai Ogini Olaposi a matsayin Sakataren riƙo da wasu sauran mutum goma sha Takwas.
A lokacin zaman da ya gudana a dakin taron masaukin baƙi na Rockview da ke birnin Legas an buƙaci membobin jam’iyyar da su kaɗa kuri’ar amincewa kan matakin.
Da ya ke jawabi, bayan kammala taron ga manema labarai, yau Talata, Sakataren Kwamitin Aminitattun, Babayo Muhammad Abdullahi, ya zargi sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da yi wa jam’iyyar zagon kasa da sauran wasu laifuka da suka sabawa dokokin jam’iyyar.
