Zaben Osun: Oyetola Ya Shigar Da Kara Mai Shafuka 1,240 Gaban Kotu.
Dan takarar gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola, ya shigar da kara mai shafuka 1,240 a gaban kotun jihar dake Osogbo.
Oyetola, wanda shine dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a zaben ranar 16 ga watan Yuli, ya je kotun ne domin kalubalantar ayyana Sanata Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta yi a matsayin wanda ya yi nasara, inji majiyar jaridar Popular News Hausa ta Sunnews.
Oyetola da Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Prince Gboyega Famodun ne suka sanya hannu a takardar ƙarar.
Jam’iyyar APC dai ta yi nuni da cewa za ta tunkari kotun don kalubalantar zaben, inda ta ce tawagar lauyoyin jam’iyyar ta ba su tabbacin cewa suna da nasara.
Da aka tuntubi babban lauyan jam’iyyar APC, Rasheed Adegoke SAN, ya tabbatar wa jaridar Sun cewa an shigar da karar ne tare da bayyana fatan jam’iyyar za ta yi nasara a kotun.
Adegoke SAN a baya ya bayyana cewa kimanin lauyoyi 50 da suka hada da Saka Layonu SAN ne suka nuna aniyar zuwa kotun don Oyetola da APC.
